Manoman shinkafa na zanga-zanga bisa shigo da shinkafa da gwamnati zatayi

Manoman shinkafa na zanga-zanga bisa shigo da shinkafa da gwamnati zatayi

- Manoma a Kebbi na zanga zanga-zanga kan bari a shigo da shinkafa

- Ance jiragen ruwa makare da shinkafa sun iso Legas

- A da dai gwamnati ta rufe boda da iyakoki domin kar a sake shigo da shinkafa daga waje

A jihar Kebbi, cibiyar noma shinkafa a Najeriya, manoma sun zo wuya kan labarin wai gwamnati ta bude bodar teku domin a shigo da shinkafar kasar waje, bayan alkawurra a baya na cewa baza a sake barin shinkafar kasar waje isowa cikin gida Najeriya ba, bayan kuma sun noma nasu sun kai kasuwa.

LAKE rice dai ita ce shinkafar da gwamnati ke tinkaho da ita, kuma ana noma ta ne a ihar Kebbi mai rafin ban ruwa da yawa, hadin kan gwamnatocin tarayya da jihohin Legas da Kebbi ya ba manoma damar noma shinkafar mai daukar ido.

KU KARANTA KUMA: Muna bukatar shugabanni masu tsoron Allah a Najeriya – Femi Fani-Kayode

Manoma shunkafa na zanga-zanga bisa shigo da shinkafa da gwamnati zatayi

Manoma shunkafa na zanga-zanga bisa shigo da shinkafa da gwamnati zatayi

A jin cewa wai an kawo shinkafa jirgin ruwa uku, manoma sun harzuka sun suka fita zuwa fadar gwamnati don kai kokensu. Gwamna Atiku Bagudu ya karbe su ya kuma saurari kokensu, ya kuma yi alkawarin mika kokensu sama, don maganin abun da ke damunsu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sanata Shehu Sani ya lissafa wasu muhimman matakai daya zama wajibi a ɗauka don sake raya Arewa

Sanata Shehu Sani ya lissafa wasu muhimman matakai daya zama wajibi a ɗauka don sake raya Arewa

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel