Muna bukatar shugabanni masu tsoron Allah a Najeriya – Femi Fani-Kayode

Muna bukatar shugabanni masu tsoron Allah a Najeriya – Femi Fani-Kayode

- Fani-Kayode ya ce Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah don ci gaba

- Tsohon ministan ya kara da cewa shugaban kasar mugu ne

A ranar Laraba, 24 ga watan Mayu tsohon ministan kula da sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode ya bukaci shugabannin Najeriya da suyi koyi da tsarin shugabancin Donald Trump gurin kula da al’amuran kasar

A yayinda yake magana a gurin kaddamar da wani littafi, tsohon ministan ya bayyana cewa Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah kafin ta ci gaba.

Mai ba tsohon ministan shawara na musamman a kafofin watsa labarai Jude Ndukwe ne ya rubuta littafin mai suna "The Vanity of 'Change' and the Audacity of Truth".

KU KARANTA KUMA: Bashin da Gwamnatin Buhari ke karbowa na nema yayi yawa-Inji CBN

Tsohon ministan ya ce matsalolin Najeriya da kalubalen da take fuskanta ba zai gushe ba har sai ta samu shugabanci na tsoron Allah.

Muna bukatar shugabanni masu tsoron Allah a Najeriya – Femi Fani-Kayode

Femi Fani-Kayode ya ce Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah

Da yake kai hari ga shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ke samun kulawar likita a birnin Landan ya ce: "Janar Muhammadu Buhari ya kasance mugun mutun da baya nufin kowa da alkhairi.

“Sannan kuma ina wasu wahayi a a nan cewa idan kasar nan ta sake kuskuren zabar shi a matsayin shugaban kasa ko kuma ta bari ya kuma bari ya zamo shugaban kasa zamuyi danasani saboda za’a kare a annoba."

Har ila yau da yake magana a kan sabon aikin sa, Ndukwe ya ce, littafin ya hada da dukkan kasidun da ya rubuta a baya game da shugabanci a Najeriya.

Ndukwe ya ce gwamnati mai ci ta dada tabarbarar da al’amuran Najeriya tun bayan ta karbi mulki a watan Mayu 2015.

KU KARANTA KUMA: Abin da Obasanjo ya fadawa Malaman sa bayan ya koma aji

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa tsohon ministan yayi kira ga shugaban kasa da ya yi murabus sannan kuma ya mika mulki ga mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Fani-Kayode ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na bukatar ya kula da kansa da kuma lafiyarsa yayinda ya bar al’amuran kasa a hannun Osinbajo.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan yadda ‘Yan Najeriya suka maida martani ga dattawan Arewa game da zaben shugabanci na 2019

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis
NAIJ.com
Mailfire view pixel