"Ba wasu 'yan matan Chibok da aka sace, duk wasan kwaikwayo ne" - Inji Labour Party

"Ba wasu 'yan matan Chibok da aka sace, duk wasan kwaikwayo ne" - Inji Labour Party

- Jam'iyyar Adawa ta Leba Party, ta zargi gwamnati da kitsa satar 'yan matan Chibok don cimma burin kawar da tsohuwar Gwamnati

- An dai ceto da yawa daga cikin 'yan matan, wasu kuma an bda rahoton rasuwarsu

- Har yau ba'a ji hira da wadanda suka kubuta a baya-bayan nan

Shugaban jam'iyyar Labour na kasa, Mal. Abdulkadir Abdussalami, ya kunno wutar zargi da wasu suka dade suna yi kan batun 'yan matan Chibok da aka ceto daga Sambisa, a hannun 'yan ta'addan Boko Haram, yace sam sam ma ba'a sace yaran ba tun usuli, makarkashiya ce kawai masu son kawar da Goodluck Jonathan daga mulki suka hada.

"Ba wasu 'yan matan Chibok da aka sace, duk wasan kwaikwayo ne" - Inji Labour Party

Tutar Labour Party

Ya kara da cewa, ai sam abun bayyi kama da hankali ba, ace sai wannan gwamnatin ce ta iya gano inda matan suke, kuma ma ta ceto su, ya kuma ce 'muje zuwa, watan Mayu na badi zasu sako sauran domin su sake cin zabe mai zuwa'.

Shugaban LP din dai, yana wannan zargi ne kamar yadda wasu ke ta yi, ciki harda shugaban tada kayar baya ta MEND, mujahid Asari Dokubo, wanda shima yace su Buhari ne suka boye yaran.

"Ba wasu 'yan matan Chibok da aka sace, duk wasan kwaikwayo ne" - Inji Labour Party

"Ba wasu 'yan matan Chibok da aka sace, duk wasan kwaikwayo ne" - Inji Labour Party

A shafukan yada zumunta na zamani ma dai, wasu 'yan Najeriya kan yi irin wannan zargi, cewa dirama ce kawai ta rena wa mutane hankali kan batun matan chibok. Abun tambaya a nan shine, ina su 'yan matan da aka ceto suke? Kuma yaushe zasu fito a zanta dasu?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel