Bashin da Gwamnatin Buhari ke karbowa na nema yayi yawa-Inji CBN

Bashin da Gwamnatin Buhari ke karbowa na nema yayi yawa-Inji CBN

– Bashin da Gwamatin Najeriya ke ci yayi yawa Inji CBN

– A cewar CBN din an ci iya abin da ya kamata wannan shekarar

– Najeriya dai na fama da matsin tattali

Bankin CBN na tsoron cewa bashin da Najeriya ta ci zai zarce matakin da ya kamata.

CBN na cewa bai dace a kara karbo bashi ba sai wata shekara.

Gwamnan babban bankin yayi wannan gargadi.

Bashin da Gwamnatin Buhari ke karbowa na nema yayi yawa-Inji CBN

Shugaba Buhari da Gwamnan CBN

Godwin Emefiele ya nuna jin tsoron sa wajen irin bashin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ke karbowa. A cewar Gwamnan bai kamata yanzu Gwamnati ta kara cin wani bashi ba don a wuce adadin abin da ya dace a karba.

KU KARANTA: Dala ta motsa a jiya zuwa N370

Bashin da Gwamnatin Buhari ke karbowa na nema yayi yawa-Inji CBN

Ministocin kudi da na kasafi

Babban bankin kasar na CBN ya bayyana cewa irin bashin da Najeriya ke ci yayi yawa kwarai da gaske hakan ma ta sa abubuwa su ka zo kasa da yadda ake tsammani. Alkaluman shekarar dai sun nuna cewa abubuwa sun ja baya.

Idan ba ku manta ba jiya kun ji cewa jimilar tattalin arzikin kasar watau GDP ya kara tsukewa da kashi 0.52%. Najeriya dai na cikin wani mugun matsi na tattalin arziki a halin yanzu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Abubuwa sun sukurkuce a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel