Dan majalisar tarayya ya sauya sheka, ko hakan baya nufin ya rasa kujerarsa?

Dan majalisar tarayya ya sauya sheka, ko hakan baya nufin ya rasa kujerarsa?

- Ana sake samun baraka a jam'iyyar adawa ta PDP

- Ana ta gudun hijira zuwa 'jirgin annabi Nuhu' dab da zabuka

- A doka kujerar majalisa na hannun jam'iyya ba wakili ba

A yau ne majalisar wakilai ta fidda sanarwa ta kafarta ta shafin twitter cewa dan majalisa mai wakiltar jami'iyyar PDP Hon. Adamu Kamale, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Hakan na zuwa ne bayan sauya sheka ta wasu a majalisar a 'yan kwanakinnan, tun bayan nasarar da tsohon gwamna Makarfi ya samu a kotun koli a batun sahihin shugaban jam'iyya.

Dan Majalisar Tarayya ya sauya sheka, ko hakan baya nufin ya rasa kujerarsa?

Dan Majalisar Tarayya ya sauya sheka, ko hakan baya nufin ya rasa kujerarsa?

A doka dai, idan ba jam'iyya ta ruguje ko rabuwa biyu ba, ba wani mai wakiltar jama'a da ke da damar sauya sheka face sai ya rasa kujerarsa.

A shekarar 2014 ma, an sami irin wannan sauyi bayan gwamnonin jam'iyya mai mulki a lokaci su biyar sun kafa jam'iyya cikin gidan PDPn, wanda hakan ya bada damar ficewa da yawa daga cikin wakilai da dattijai a majalisar, ciki kuwa harda kakakin wakilan na lokacin, Gwamna a yanzu, Waziri Tambuwal na Sakkwato.

Ko yaya wadanda wannan 'yan majalisa da suke wakilta zasu dubi wakilin nasu? Kuma yaya jam'iyyar tasa ta da PDP zata bi kadi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel