Majalisar dattijai ta tuhumi babban bankin kasa kan rashin kwandaloli a Najeriya

Majalisar dattijai ta tuhumi babban bankin kasa kan rashin kwandaloli a Najeriya

- An shafe shekaru ba'a ji duriyar kwandalaye ba

- Kudin dai bassu da ko daraja a yanzu

- An janye su bayan gano cewa wasu na narka su zuwa wasu abubuwan daban

Ba tun yau ba, an dade ana neman yadda za'a dawo da darajar Naira har ya zamo cewa za'a iya amfani da kananan kudi kamar kwabbai da sulalla, kamar dai yadda akeyi a kasashen waje, amma an kasa gano bakin zaren.

Majalisar Dattijai ta tuhumi babban bankin kasa kan rashin kwandaloli a Najeriya
Kudin kwandaloli

A da can, kananan kudi na da matukar daraja, kuma sulalla ne aka fi amfani dasu, manyan kudi na takarda sai wane da wane, amma yanzu abin ya canja sosai. Zamani yasa ba'a hada-hada da kudin karfe.

Majalisar Dattijai ta tuhumi babban bankin kasa kan rashin kwandaloli a Najeriya
Tsofin kudin Najeriya

Sanata mai wakiltar Katsina, a jam'iyyar APC, Mustafa Umar, ya yi kira ga CBN da ta gaggauta dawo da kwandalaye cikin harkar hada-hadar kasuwanci, a kasar nan.

Ya kara da cewa, ba daidai bane a ce an nemi kwandalaye an rasa gaba daya.

Su dai a nasu bangaren , babban bankin, sun janye kudaden ne saboda basu da daraja ko ta sisin kwabo, bassu da kuma farin jini, sannan kuma a cewarsu, bugo kudin na da tsada sosai, domin karafan nada daraja. Ad yawa ma dai, masu harkar karafa ke sace su suna narka su domin su mayar zuwa wani abun mai amfani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel