Bashin gaba: yan ƙabilar Tiv da Jukun sun kashe junansu sakamakon rikicin ƙabilanci

Bashin gaba: yan ƙabilar Tiv da Jukun sun kashe junansu sakamakon rikicin ƙabilanci

- Rikicin kabilanci ya kaure tsakanin wasu kabilu biyu a jihar Benuwe

- An kona gidaje sama da ashirin sakamakon rikicin

Kimanin gidaje 20 ne aka kona biyo bayan rikicin kabilanci daya kaure tsakanin yan kabilar Tiv da na kabilar Jukun a kauyen Fiidi dake hanyar zuwa filin sauka da tashin jirage dake Makurdi, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito.

NAN, ta tattaro bayanan cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon daddaden gaba dade tsakanin al’ummomin kabilun biyu, wanda yayi sanadiyyar salwantar rayukan mutane da dama, ciki har da na matafiya.

KU KARANTA: Sojoji sun lalata matatar mai ta barayin mai a Okrika

Wani shaidan gani da ido, Steven Angwe ya bayyana ma majiyar NAIJ.com cewar an fara fadan ne biyo bayan cacar baki daya kaure tsakanin wasu matashin Tiv da na Jukun a kasuwan kauyen Fiiidi akan wani fili a ranar Litinin 22 ga watan Mayu.

Bashin gaba: ƙan ƙabilar Tiv da Jukun sun kashe junansu sakamakon rikicin ƙabilanci

Gidajen da aka babbaka

Da misalin karfe 3 na yamma aka fara, har zuwa karfe 9 na safiyar ranar Talata 23 ga watan Mayu, hakan yayi sanadiyyar mutanen kauyen tserewa don kare rayukansu.

Kaakakin rundunar yansandan jihar, ASP Moses Yamu ya bayyana ma NAN cewa sun tabbatar da mutuwar mutum guda, da kona gidaje 20.

Daga karshe, Kaakakin ya kara da cewa sun kama mutane 17, kuma an girke jami’an yansanda a kauyen don tabbatar da tsaro.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Anyi tattakin yaki da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel