Sabon bincike ya nuna yawan cin tsire da balangu na kawo manyan cutuka

Sabon bincike ya nuna yawan cin tsire da balangu na kawo manyan cutuka

- Sabon bincike na masana ya kara tabbatar da illolin cin jan nama

- Sinadarin karfe na iron da jini ke bukata shi ake samu a daya daga cikin amfanin cin nama daga dabbobi

- An shafe shekaru 17 ana binciken. An kuma bi diddigin wadanda ake biciken da rayuwarsu don sanin abincinsu tsawon lokacin

Sabon bincike na masana ya kara tabbatar da illolin cin jan nama. Sinadarin karfe na iron da jini ke bukata shi ake samu a daya daga cikin amfanin cin nama daga dabbobi.

An shafe shekaru 17 ana binciken, sannan kuma an bi diddigin wadanda ake biciken da rayuwarsu don sanin me suke ci a lokutan abinci.

Jami'ar Amurka ta gudanar da binciken, an kuma sami bayanai da ke nuna cewa cutuka irinsu kansa, kiba, da hawan jini suna kama masu son cin balangu da kashi daya bisa hudu, kuma sun fi saurin mutuwa, fiye da wadanda bassu cin jan naman.

Sabon bincike ya nuna yawan cin tsire da balangu na kawo manyan cutuka.
Sabon bincike ya nuna yawan cin tsire da balangu na kawo manyan cutuka.

KU KARANTA KUMA: Najeriya na cikin yanayi mai iya tarwatsewa – Obasanjo

Masu cin nama kamar na kifi da kaji, farin naman, sun fi samun yar tazara da tsawon rayuwa, musamman in sun hada da atisaye da cin kayan ganye da 'ya'yan itatuwa.

Masana dai sun gano cewa, sinadarin iron da ke jini shi ne jikin mutum yake bukata idan yaci nama, shi kuma ba safai ake samunsa daga itatuwa ba, shi yasa dole ana bukatar nama amma ba da yawa ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Har yanzu kana shan lemun kwalba?

Asali: Legit.ng

Online view pixel