Yan kallo sun lakaɗa ma alkalin wasa dukan kawo wuƙa

Yan kallo sun lakaɗa ma alkalin wasa dukan kawo wuƙa

- Alkalin wasa ya gamu da fushin yan kallo a kasar Zimbabwe

- Yan kallon sun yi masa dukan tsiya inda suke zarginsa da hura musu faca

Wani alkalin wasa ya gamu da fushin yan kallo a filin wasa na Kwekwe dake kasar Zimbabwe bayan ya kyale wata kwallo da aka zura ta hanyar satar fagge.

Rahotanni sun bayyana cewar alkalin wasan mai suna Thomas Kusosa ya ci dukan tsiya a hannun magoya bayan kungiyar Highlander FC da basu gamsu da busan da yayi musu ba.

KU KARANTA: Yansanda sun kama mai fataucin sassan mutum a jihar Kebbi

Majiyar sun bayyana ma NAIJ.com cewar wasan anyi shi ne tsakanin Highlander da Dynamos a garin Bulawayo.

Yan kallo sun lakaɗa ma alkalin wasa dukan kawo wuƙa

Alkalin wasan

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewar magoya bayan Highlander sun cimma alkalin wasan ne a wani matattarar shan giya, inda suka bi shi da gudu, shima yace kafa mai naci ban baki ba, amma duk da haka sai da suka ishe shi, inda suka lakada masa dan banzan duka.

Da kyar dai ya sha, inda ya samu wata motar tasi tayi tsiratar da shi. Sai dai har yanzu kungiyar alkalan wasan kwallon kafa na kasar basu fitar da wata sanarwa ba, suma yansandan garin Kwekwe sun ce basu samu rahoton lamarin ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan Najeriya na atisaye

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel