Kungiyar Izala ta kafa wata kwamiti don taimakawa aikin gona

Kungiyar Izala ta kafa wata kwamiti don taimakawa aikin gona

- kungiyar JIBWIS ta sanar da komawa gona daga damunar banan nan

- Kwamishinan kudi na jihar Gombe ya ce za a inganta amfanin gona ta yadda za a fitar da kyayyakin zuwa kasashen waje

- Kungiyar tace ta nemi filaye a kowacce jiha domin mutanen da suke da sha’awar aikin gona musamman matasa marasa aikin yi

Kungiyar JIBWIS ta Ahlus Sunna a Najeriya ta kaddamar da wani kwamitin noma don taimakawa matasa wajen dogaro da kai da kuma bunkasa aikin noma.

Wannan shirin dai na nuna kara sauya hanyoyin samun kudin gudanarwa a tsakanin kungiyoyin addini a Najeriya, kungiyar JIBWIS ta sanar da komawa gona daga damunar banan nan.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, kungiyar wadda kan samu tallafi daga taimakon mutane musamman ma a masallatai inda tun farko ta kirkiro wani shirin tallafawa marayu da miskinai ta hanyar sayan katin waya da aka tura daga naira 100 mai suna Manara, a halin yanzu ta kaddamar da kwamitin noma don dogaro da kai.

Kungiyar Izala ta kafa wata kwamiti don taimakawa aikin gona

Zaman kaddamar da kwamitin noma na kungiyar JIBWIS

KU KARANTA KUMA: Kaji abunda 'yayan marigayi Ado sukace game da tsomomuwar da Sarki Sanusi ke ciki

Shugaban kwamitin kuma kwamishinan kudi na jihar Gombe, Alhaji Hassan Mohammed ya ce za a inganta amfanin gona ta yadda za a fitar da su kasashen waje, ba wai kawai amfani da su a cikin gida ba.

Alhaji Hassan ya ce za a nemi karin filayen noma akan wadanda ake da su a yanzu, ya kuma tabbatar da cewa za a inganta noman ta yadda zai bayar da sha’awa.

Kungiyar JIBWIS za ta nemi filaye a kowacce jiha domin mutanen da suke da sha’awar aikin gona musamman matasa marasa aikin yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon direban Bishof David Abioye wanda ya karbi musulunci yayin da ya yi murabus da cocin Living Faith Church

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel