Yansanda sun kama mai fataucin sassan mutum a jihar Kebbi

Yansanda sun kama mai fataucin sassan mutum a jihar Kebbi

- Yansanda a jihar Kebbi sun cika hannu da wani mutumi daya kware wajen hakar kaburbura yana sace gawa

- Mutumin yace talauci da halin matsin rayuwa ne ya shigar da shi wannan harka

Jami’an hukumar yansandan jihar Kebbi sun cika hannu da wani mutumi daya kware a sana’ar ciro gawa daga kabari, kuma ya yanke sassan jikinta don fataucinsa a garin Bagudu na jihar Kebbi.

Kwamishinan yansandan jihar, Ibrahim Kabiru ya bayyana haka yayin dayake ganawa da yan jaridu a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu, inda yace sun samu nasarar kama mutumin ne bayan samun wani rahoton sirri, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

KU KARANTA: Kasar Qatar ta kere sa’a, ta gina filin wasan ƙwallon ƙafa mai na’uran sanyaya ɗaki

Kwamishinan yace da misalin karfe 3:30 na dare ne suka kama mutumin a makabartan Kaoje yayin dayake kokarin hako wani gawar bawan Allah don siyar da sassan jikinta.

Yansanda sun kama mai fataucin sassan mutum a jihar Kebbi

Mai fataucin sassan mutane

Kwamishinan ya kara da fadin, mutumin ya amsa laifinsa, kuma ya fallasa mutumin daya daura shi a harkar, mai suna Malam Muhammadu dake zama a jihar Sakkwato, inda shi mutumin ke kai katako kafin ya shiga wannan harkar.

Daga karshe dai mutumin ya nemi afuwa, inda yace talauci ne ya sanya shi yin wannan mummunar aiki, tare da burinsa na ganin ya kula da iyalinsa.

A wani labarin kuma, NAIJ.com ta gano yansanda sun kama wani fasto mai shekatu 55 mai suna Alimi Isaiah dauke da kawunan mutane da wasu kayan tsafe tsafe a jihar Ogun.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Guragun Najeriya sun koka

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel