Gwamnatin tarayya ta shirya ba kananan 'yan kasuwa lamunin naira biliyan 150

Gwamnatin tarayya ta shirya ba kananan 'yan kasuwa lamunin naira biliyan 150

- Gwamnatin tarayya Najeriya ta shirya ba kananan 'yan kasuwa lamunin wadda zai taimaka wa ‘yan kasuwar wajen bunkasa sana’o’in su

- Gwamnan jihar Bauci ya kaddammar da shirin gwamnatin tarayyar na yankin Bauchi

- Gwamnan ya ce mutanen jihar Bauchi 40,000 ne zasu amfana daga lamunin

Gwamnan jihar Bauci ya ce rancen za'a baiwa 'yan kasuwan da ada can suna cikin kasuwanci amma saboda canje-canjen yanayi watakila jarinsu ya fara komawa baya

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, gwamnan Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar yayin da yake kaddammar da shirin na yankin Bauchi ya ce gwamnatin tarayya ta fito da shirin taimakawa kananan 'yan kasuwa wadanda jarinsu bai kai ba, ko kuma dama can basu da jarin na cigaba da kasuwanci.

Gwamnan ya ce rancen za'a baiwa 'yan kasuwan da ada can suna cikin kasuwanci amma saboda canje-canjen yanayi watakila jarinsu ya fara komawa baya.

Irin mutanen ne za'a tallafawa domin su bunkasa jarinsu samu su fadada kasuwanci.

A jihar Bauchi mutane 40,000 ne zasu amfana daga lamunin. A bankin masana'antu na kasa nan ne gwamnatin tarayya ta ajiye kudaden mai yawan naira biliyan 150 saboda a rabawa 'yan Najeriya.

Lamunin dai bashi da ruwa. Abun da aka ba mutum shi ne zai mayar cikin watanni 6. Gwamnan ya ce dole a yi hattara domin ba bashin da mutum zai dauka ba ne, ya je yana kara mata.

Alhaji Mansur Manusoro mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi a kan kungiyoyi da masana'antu ya yi bayani akan matsayin gwamnatin jihar dangane da shirin samar da lamunin.

KU KARANTA KUMA: Uwargidar shugaba Buhari ta kaddamar da gina asibiti a Daura Read

Inji Alhaji Mansur suna aiki da bankin masana'antu da kuma hukumar da aka dorawa alhakin tantance masu sana'a kafin a basu kudi. Rance mafi kankanci shi ne naira 10,000 mafi yawa kuma 100,000.

Duk wanda ya kasa biyan bashin shugabannin kungiyarsa za'a kama su biya.

Wasu da suka amfana da lamunin sun tofa albarkacin bakinsu. Wata da take sana'ar sayar da ruwa da yin zoborodo ta samu 50,000 ta ce kudin zai taimaka mata bunkasa sana'ar. Sun kuma amince da tsarin biyan bashin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya ce zai kara da shugaba Buhari a zaben shugaban kasa na 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel