Kotu ta tura shugaban jam'iyar PDP na Jihar jigawa zuwa gidan yari

Kotu ta tura shugaban jam'iyar PDP na Jihar jigawa zuwa gidan yari

- Wani kotun majistare da ke jihar Jigawa ta tura shugaban jamiyyar PDP na jihar da wasu tsaffin makarraban gwamnatin jihar Jigawa zuwa gidan yari

- Ana zargin shugaban jamiyyar da kuma sauran mutanen da aikata wasu lefuka 4

- Alkalin kotun ya dage sauraren karar zuwa ranar 23 ga wannan watan

Kotun Majistare ta biyu dake zaman ta a birnin dutse jihar Jigawa ta tura shugaban jamiyyar mai adawa PDP na jihar Alhaji Salisu Mahmuda da wasu tsaffin makarraban gwamnatin jihar Jigawa su 5 zuwa gidan yari har zuwa ranar 23 ga wata Mayu domin yanke hukunci a kan bukatar bada belinsu kamar yadda lawyoyi suka bukata.

Ana zargin Alhaji Salisu Mahmud tare da tsaffin kwamishinoni 5 da jam'ian kungiyar shugabannin ma'aikatan kananan hukumomi ta ALGON da aikata lefuka 4, wadanda suka musanta.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, sauran wadanda ake tsare dasu tare da shugaban jamiyyar ta PDP sun hada da tsaffin kwamishinonin kananan hukumomi Salisu Saleh Indirawa da Nasiru Umar Roni da Shehu Umar Chamo da tsoffin shugabannin kananan hukumomin Gagarawa Mukhtar Ibrahim Gongal da na Kirikasamma Abba Mohammed Daguro.

Ana zargin sune da cin amanar gwamnati wanda hakan ya sabawa sashe na 97 da 312 da 123 da Kuma na 287 na dokar Final Code.

KU KARANTA KUMA: Turawa na taya Shugaba Buhari fatan samun sauki

Duk da yake sun musanta zarge-zargen, lauyan mutanen Barista Yakubu Abdullahi Rubah ya nemi belinsu tun da yake yansanda ne suka gayyaci mutanen kuma suka amsa gayyatar. Amma alkalin kotun mai sharia Usman Muhammed Lamin ya dage sauraren karar zuwa ranar 23 ga wannan watan da muke ciki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel