Uwargidar shugaba Buhari ta kaddamar da gina asibiti a Daura

Uwargidar shugaba Buhari ta kaddamar da gina asibiti a Daura

- Aisha Buhari ta kaddamar da gina wata asibiti a garin Daura da ke jihar Katsina domin kiwon lafiyar mata da yara

- Matar shugaban kasar ta ce zata gina asibitin ne domin agaza wa marasa galihu da miskinai a kasar baki daya

- Uwargidar mukaddashin shugaban kasar, Dolapo Osinbajo ta yaba wa Aisha Buhari a kan sadaukar wajen kyautata yanayin marasa galihu

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari ta kaddamar da gina wata asibiti mai gado 50 a ranar Alhamin, 18 ga watan Mayu a garin mijinta da ke Daura a jihar Katsina domin kiwon lafiyar mata da kuma yara.

Da take jawabi a lokacin kaddamar da gina a babban asibitin, Daura, Aisha Buhari ta ce zata gina asibitin ne domin agaza wa marasa galihu da miskinai a fadin kasar.

NAIJ.com ta ruwaito zewa, za a gina asibitin ne a karkashin shirin uwargidar shugaban kasa Aisha Buhari wadda aka sani da ‘Future Assured’ a matsayin wani bangare na taimako don rage mace-macen masu juna biyu da kananan yara a kasar.

Uwargidar shugaba Buhari ta kaddamar da gina asibiti a Daura

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari a lokacin kaddamar da gina asibiti a Daura

Aish Buhari, duk da haka dai ta yi alkawarin gina irin wannan asibiti a sauran yankuna 6 na kasar.

KU KARANTA KUMA: Mukaddashin shugaban kasa ya gana da shugaban INEC

Dolapo Osinbajo wanda ita ce uwargidar mukaddashin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ta rufe wa Aish Buhari baya zuwa wajen bikin ta yaba wa matar shugaban kasar a kan sadaukar wajen kyautata yanayin marasa galihu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin ya kamata shugaba Buhari ya mika wa mataimakin shugaban kasar Osinbajo mulki saboda kan al'amurran da suka shafi kiwon lafiyasa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel