Turawa na taya Shugaba Buhari fatan samun sauki

Turawa na taya Shugaba Buhari fatan samun sauki

– Wani Bature ya kai sakon sa gidan Shugaban kasa da ke Landan

– Baturen na fatar Shugaba Buhari ya samu lafiya

– Kusan mako biyu kenan da Shugaba Buhari ya bar kasar

An ga wani Bature dauke da fulawa a gidan shugaban kasa.

Baturen yana fata shugaban Najeriya ya samu sauki.

Jaridar Guardian ta bayyana wannan labari.

Turawa na taya Shugaba Buhari fatan samun sauki

Shugaba Buhari na fama da rashin lafiya a Ingila

A Ranar Laraba ne wani Bature ya tashi ta-ka-nas har gidan Shugaban kasar Najeriya da ke Landan inda ya ajiyewa Shugaba Buhari takardar fatan samun lafiya da kuma wasu ‘yan fulawowi.

KU KARANTA: Kasar Ingila ta yabawa kokarin Shugaba Buhari

Turawa na taya Shugaba Buhari fatan samun sauki

Ana wa Shugaba Buhari fatan samun sauki

Shugaban Najeriyar dai yana fama da rashin lafiya wanda har yanzu ba a bayyanawa mutane abin da ke damun sa ba. Yayin da yake Landan har wasu sun fara jita-jitar cewa ya rasu sai ga shi dai Turawa na masa fatar samun sauki.

Wani tsohon Ministan PDP Femi Fani-Kayode yace yana jin tsoro za a hambarar da Gwamnatin kasar a dalilin rashin lafiyar shugaba Buhari. Haka kuma yace za a nemi mataimakin sa Yemi Osinbajo yayi murabus da karfi da yaji.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda mu ka yi da Buhari Inji Femi Fani-Kayode

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel