Wasu abubuwa sun fashe a jami'ar Maiduguri

Wasu abubuwa sun fashe a jami'ar Maiduguri

- Yan ta’addan Boko Haram sun kuma kai hari jami’ar Maiduguri

- Wata ‘yar kunar bakin wake mace ce ta kai harin

- Abun ya yi mugun shafar daya daga cikin masu gadin jami’ar

Wasu ‘yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram sun kai hare-hare har sau biyu a jami’ar Maiduguri (UNIMAID) inda suka bar mai tsaron jami’ar da mummunan rauni.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an kaddamar da harin ne a daren ranar Alhamis, 18 ga watan Mayu da kuma safiyar ranar Juma’a, 19 ga watan Mayu.

Abu Babati shugaban dalibai na jami’ar ya tabbatar da harin.

KU KARANTA KUMA: Dattawa sun maida martani game da kalaman gwamnan jihar Taraba

Ya ce wani soja ya dakile daya daga cikin yan kunar bakin waken a kusa da sashin karatun liktancin dabobbi sannan kuma an harbe shi bayan ya tayar da bam din sa.

Dayan harin ya afku ne a kusa da dakin kwanan dalibai mata na BOT a safiyar ranar Juma’a.

Yusuf Ibrahim wanda ya kasance dalibi a jami’ar UNIMAID ya ce wani mai tsaron dakin kwanan daliban ya ji mugun rauni sannan kuma ya shiga halin gigita bayan harin.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa wani hari makamancin haka ya afku a jami’ar lokacin da daya daga cikin maharan ya shiga jami’ar ta kofar baya da kudirin shiga makarantar kafin sojan dake tsaro ya aika shi lahira.

NAIJ.com ta kuma samu labarin cewa jami’in hulda da jama’a na makarantar Mista Tanko Ahmed ya tabbatar da mummunan harin a jami’ar.

Kakakin ya ce al’amarin ya afku ne da misalin karfe goma sha daya na dare (11pm) ranar Lahadi 9 ga watan Afrilu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar sojin saman Najeriya na ci gaba da yakar yan ta'addan Boko Haram.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel