Matakan kare kamuwa da ciwon hawan jini guda 6

Matakan kare kamuwa da ciwon hawan jini guda 6

- Likitoci sun shawarci jama'a akan yawan motsa jiki don maganin hawan jini

- Likitocin sun gargadi jama'a akan illolin cutar haan jini

Wasu kwararrun likitoci sun shawarci mutanen Najeriya akan yadda za su kulaw da lafiyarsu domin guje ma kamuwa da cutar hawan jini, inji rahoton jaridar Premium Times Hausa.

Likitocin sun bada wannan shawaran ne a taron ranar wayar da kan al’umma game da cutar hawan jini wanda a ke yi a ranar 17 ga watan Mayun kowane shekara.

KU KARANTA: Za’a fara aikin shimfiɗa layin dogo daya haɗe Kano-Zaria-Kaduna

Likita Ogah Okechukwu yace cutar hawan jini na daya daga cikin cututtukan da ke yin sanadin mutum farar daya, ba tare da dogon jinya ba.

Matakan kare kamuwa da ciwon hawan jini guda 6
Likita da mara lafiya

Bincike ya nuna cewa mazaunan yankin arewa maso yammacin Najeriya sun fi kamuwa da cutar hawan jini sannan kuma cutar ta fi kama maza fiye da mata. Sai dai wani abin takaici da majiyar Legit.ng ta gano shine, cutar bai kyalle matasa ba musamman daga shekara 25 zuwa sama.

A wani bincike da hukumar kiwon lafiya ta duniya tayi, ta gano cutar hawan jini ta fi kama bakaken fata fiye da turawa, a bakaken fatar ma, ta fi kama talakawa.

Okechukwu ya shawarci mutane akan hanyoyin da za su iya bi da kiyayewa domin gujewa kamuwa da cutar kamar haka:

1. Yawaita motsa jiki

2. Rage cin kitse

3. Yawaita cin kayan marmari da ganyayyaki

4. Rage cin gishiri

5. A guji shan taba sigari da giya

6. Yawaita zuwa Asibiti don yin gwajin hawan jini

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya dace Buhari ya mika ma Osinbajo mulki?

Asali: Legit.ng

Online view pixel