Bincken Sarkin Kano: Anyi cacar baki tsakanin majalisar dokokin Kano da majalisar wakilai

Bincken Sarkin Kano: Anyi cacar baki tsakanin majalisar dokokin Kano da majalisar wakilai

- Kaakakin majalisar dokokin jihar Kano ya gargadi majalisar wakilai data daina shiga aikinsu

- Rurum ya gargadi majalisar wakilai ne da kada ta tsoma musu baki a binciken da suke yi ma Sarkin Kano

Kaakakin majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya ja kunnen majalisar wakilai na tarayya data daina shiga sharo ba shanu a cikin lamurran majalisar.

Rurum ya gargadi majalisar wakilai ne da kada ta tsoma musu baki a binciken da suke yi ma Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, inda yace majalisar wakilai bata da hurumin yi mata katsalandana harkokinsu a matsayinsu na yan majalisar dokokin jihar Kano.

KU KARANTA: Arzikin Dangote, TY Danjuma, Otedola, Adenuga da Alakija zai iya magance talauci a Najeriya

Alhassan Rurum ya bayyana haka ne ga jaridar Daily Trust a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu inda yake mayar da martani ga majalisar wakilai, bayan wani dan majalisar Aliyu Sani Madakin Gini yayi kira ga majalisar data sanya baki a binciken da majalisar dokokin jihar Kano take yi ma Sunusi.

Bincken Sarkin Kano: Anyi cacar baki tsakanin majalisar dokokin Kano da majalisar wakilai

Sarkin Kano

A ra’ayin Madakin Gini, muddin aka bari majalisar dokokin jihar Kano ta cigaba da binciken Sarkin, toh tabbas hakan zai iya kawo rudani a jihar Kano.

Idan ba’a manta ba, NAIJ.com ta ruwaito wano dan majalisar dokokin jihar dake wakiltar karamar hukumar Nassarawa Ibrahim Gama ya gabatar da wata kudiri inda yake bukatar a binciki sarkin Kano kan wasu tuhume tuhume guda takwas da yake zargin Sarkin dasu.

Bincken Sarkin Kano: Anyi cacar baki tsakanin majalisar dokokin Kano da majalisar wakilai

Kaakaikn majalisar dokokin jihar Kano

Hakan ya sanya majalisar kafa wani kwamitin bincike na mutum 7 don duba lamarin, tare da bayar da rahoto ga majalisar a cikin sati biyu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Saurari Sarki Sunusi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel