Yan Najeriya 4000 gwamnati ta ceto daga hannun Boko Haram – Minista

Yan Najeriya 4000 gwamnati ta ceto daga hannun Boko Haram – Minista

- Zuwa yanzu Najeriya ta ceto sama da mutane 4000 da Boko Haram tayi garkuwa dasu

- Ministan tsraao yace akwai bukatar samun dangantaka kyakkyawa tsakanin jami’an tsaro da al’umma

Ministan tsaron Najeriya, Mansur Dan- Ali ya bayyana cewar zuwa yanzu gwamnatin Najeriya ta ceto sama da mutane 4000 da Boko Haram tayi garkuwa dasu, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Dan Ali ya bayyana haka ne a aranar Alhamis 18 ga watan Mayu yayin wani taron kara ma juna sani kan dangantaka tsakanin sojoji da al’ummar gari don samar da tsaro, inda yace:

KU KARANTA: Kasar Kamaru ta fatattako yan gudun hijira fiye da 10,000 zuwa Borno

“Sama da mutane 4000 gwamnatin Najeriya ta kubutar daga hannun kungiyar Boko Haram, ciki har da yan matan Chibok 106 da aka sace a shekarar 2014.

“Amma idan ana bukatar samun muhimman nasarori a bangaren tsaro, sai an samu dangantaka kyakkyawa tsakanin jami’an tsaro da al’umma, tare da amininci da girmama juna tsakanin bangarorin biyu.”

Yan Najeriya 4000 gwamnati ta ceto daga hannun Boko Haram – Minista

Sojoji tare da wadanda aka ceto

Ministan Dan Ali ya bayyana kokarin dakarun sojin kasar nan wajen murkushe kungiyar ta Boko Haram a matsayin dalilin daya sanya Boko Haram basa iya kai hare hare kamar yadda suka saba, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Filato ya bayyana muhimmancin wannan taro, inda yace yazo akan gaba, daidai lokacin da ake bukatar sa, gwamnan ya kara da cewa sakamakon halin rashin tsaro da jihar Filato tayi fama da shi, sun fahimci amfanin kyakkyawar alaka tsakanin Sojoji da farar hula.

Dayake nasa jawabin, Kaakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya shawarci jami’an soji da kada su dinga amfani da damar su sun cin zarafin al’umma, Dogara yace:

“Don kana rike da bindiga, ko mukamin soji bai kamata ka yi tunanin kafi kwoa ba, kamata yayi ace kana kankantar da kanka, suma farar hula ya dace su girmama jami’an tsaro.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicn Boko Haram, kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel