Kwanan nan Za a fara aikin layin dogo na Kano-Zaria-Kaduna

Kwanan nan Za a fara aikin layin dogo na Kano-Zaria-Kaduna

- An kusa share zamani guda ba'a harkar layin jirgin kasa a Arewacin Najeria, diga da aka yi tun zamanin mulkin mallaka na turawa.

- An sami babban hobbasa daga gwamnati wajen dawo da safara ta harkar jirgin kasa a Najeriya, inda aka zuba makudan daloli.

- Shugaban NRC, hukumar jirgin kasa ta kasa ya kai ziyara fadar Sarkin Zaria.

A jiya ne Sarkin Zaria, Alh. Shehu Idris, ya karbi tawagar Shugaban hukumar harkokin safara ta jiragen kasa, a fadarsa dake birnin Zazzau.

Tawagar ta hada da Alhaji Usman Abubakar, Shugaban NRC na kasa, wanda ya tabbatar cewa, a kwanan nan ne za'a fara aikin sabon layin dogo na Zamani, wanda zai hade da hanyar jirgi da ta taho daga Abuja babban birni zuwa Kaduna garin Gwamna. Digar jirgin zata tashi ne daga Kaduna, tabi ta ZAria, ta isa Kano.

Shugaban, ya bada tabbacin cewa an samar da kudin aikin, an bada kwangilar ga kwararru daga kasashen waje. Zasu kuma iso da kayan aikinsu na zamani domin fara aikin.

Kwanan nan Za a fara aikin layin dogo na Kano-Zaria-Kaduna.

Kwanan nan Za a fara aikin layin dogo na Kano-Zaria-Kaduna.

Ya kuma bada tabbacin za'a farfado da tsohuwar hanyar layin dogo da aka dena amfani da ita, inda itama za'a gyara ta. Ya kuma ce, aikin zai kawo wa samari abin yi, zai kuma habaka tattalin arziki na zaria, da ma yankin baki daya.

KU KARANTA KUMA: Wasu abubuwa sun fashe a jami'ar Maiduguri

A nasa bayanin, Mai martaba Sarkin Zazzau, Alh. Shehu Idris, ya tabbatar wa da tawagar, hadin kan jama'arsa, yayi musu fatan sa'a, ya kuma yi kira ga Gwamnatin tarayya, da ta bada isassun kudi domiun kammala aikin yadda ya kamata a kan lokaci.

NAIJ.com ta rahoto inda Sarkin, ya kuma kara da cewa, sai da irin wadannan ayyukan ne, za'a sami arziki ya zaga tsakanin talakawa. Ya kuma sanya musu da aikin albarka.

Ku biyo mu a facebook: https://facebookcom/naijcomhausa

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel