Babbar magana: Ana nema a sauke Shugaba Buhari da Osinbajo

Babbar magana: Ana nema a sauke Shugaba Buhari da Osinbajo

– An kai kara kotu domin a tsige shugaba Muhammad Buhari

– Haka kuma ana nema a sauke mataimakin shugaban kasar

– Jam’iyyar HDP tace har Ministoci a sauke

Wata Jam’iyyar adawa ta nemi a tsige shugaban kasa da Mataimakin sa.

Haka kuma Jam’iyyar na nema a sauke kaf Ministocin kasar.

Ana karar cewa Jam’iyyar APC ta kashe fiye da kudin da aka kayyade na kamfe.

Shugaba Buhari da Osinbajo

Shugaban=Buhari da Mataimakin sa Osinbajo da Ministoci

Jam’iyyar nan ta Hope Democratic Party, HDP ta nemi Kotu ta soke zaben shekarar 2015 da Jam’iyyar APC tayi nasara. A cewar ta Jam’iyyar ta saba doka inda ta kashe kudi fiye da yadda doka ta tanada na yakin neman zabe.

KU KARANTA: Majalisa ta gargadi Ministan mai Ibe Kachikwu

Hakan ya sa Jam’iyyar ta nemi Kotu ta soke zaben a kuma sauke shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo. Bugu-da-kari Jam’iyyar ta nemi a rushe kaf Majalisar Ministocin kasar.

Shugaban kasa na rikon-kwarya ya fara aiki kan kasafin kudin bana Inji mai magana da bakin sa Laolu Akande. Idan ba a manta ba jiya Mukaddashin shugaban kasa ya zauna da Ministocin tattalin arziki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Femi Fani Kayode ya fadi yadda su ka yi da Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel