Daukar sabbin matakai kan sarkin Kano ba dai-dai bane - Inji Bafarawa

Daukar sabbin matakai kan sarkin Kano ba dai-dai bane - Inji Bafarawa

- Bafarawa ya yi tir da daukar sabbin matakai kan mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu

- Majalisar dokoki ta jihar Kano ta kafa kwaitin bincike akan mai martaba Sarkin Kano da majalisar masararutar Kano

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalahatu Bafarawa, ya ce daukar sabbin matakai kan mai martaba sarkin Kano Sanusi bayan sulhu da gwamnoni suka yi kan lamarin a Kaduna ba dai-dai ba ne.

Bafarawa da ke magana da manema labarai a Abuja, ya ce karin mataki ko neman kwabe sarkin zai rage darajar sarauta ne da hadin kan arewa.

Ya ce: “Abin kunya ne garemu ‘yan arewa ace yau a majalisar jihar Kano ana binciken sarkin Kano.”

Daukar sabbin matakai kan sarkin Kano ba dai-dai bane - Inji Bafarawa

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ayarinsa

KU KARANTA KUMA: Sanusi yayi hayan lauyoyi masu karfi 3 do dakatar da shirin tsigiyar da akayi masa

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Bafarawa ya ci gaba da cewa idan har gwamnonin arewa su 4 zasu je su zauna da gwamnan Kano, kuma sarkin Kano a gwada masa irin kura-kuransa har ya yarda, sai a bari a ga alkawarin da yayi ko zai cika.

Majalisar dokoki ta jihar Kano dai ta kafa kwaitin bincike akan mai martaba Sarkin Kano da majalisar masararutar Kano, game da zargin kashe kudade ba tare da amincewar ita majalisar ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel