Kungiyar CAN ta nemi Najeriya ta janye daga wasannin Musulmin Duniya na BAKU 2017

Kungiyar CAN ta nemi Najeriya ta janye daga wasannin Musulmin Duniya na BAKU 2017

- Gwamnatin Najeriya ta tabbatarda cewa Najeriya na daya daga kasashe 57 da zasu halarci taron wasannin da akeyiwa suna da, “BAKU 2017”

- CAN ta nune cewa Halartan Najeriya taron Na nuna sabawa kundin tsarin Secularism da kasar ke gudanuwa akai

Kungiyar Christian Association of Nigeria (CAN) ta nuna rashin amincewa da Najeriya a tarayya da zatayi a wasannin musulman duniya Azerbaijan, ta hanyar nuna hakan ba tsari bane.

Kungiyar ta nemi gwamnati tayi gaggawar janyewa daga tarrayya a wasannin a rahoton NAIJ.com daga garesu.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatarda cewa Najeriya na daya daga kasashe 57 da zasu halarci taron wasannin da akeyiwa suna da, “BAKU 2017.”

NAIJ.com ta rawaito cewa Babban maga takardar CAN, Dr Musa Asake ne yake furucin a wasikar da ta fita a ranar litinin watan 10 ga Mayu 2017 zuwa ga mukaddasin Najeriya wato,Prof. Yemi Osinbajo (SAN), wasikar ta nuna tarayyar najeriya ya sabawa tsarin Najeriya na nuna cewa babu ruwanta da karkata ga addinanci.

A wasikar da yan jaridu suka samu ta Alhamis ta zoda matashiyar Rashin bin tsarin Najeriya gurin tarayya a wasannin duniya na musulmai NAKU, haka kuma an aika wasikun zuwa ga shugaban majalisar Zartarwa,Dr. Bukola Saraki da Sakataren Gwamnatin tarayya.

Daga korafe-korafen wasikun akwai maganar; “ya bayyana garemu BAKU 2017 zasu kaddamarda wasanninsu na hudu a shekarar 2017, a garin Azerbaijan a tsakanin 12 – 22 na watan Mayu 2017, kuma inda ta shafemu shine tarayyar Najeriya a a wasannin.

KU KARANTA: Yan Najeriya 193 ke mutuwa kowanne awanni 24 daga cutar daji – Masana

Masu Jibintar lamarin sun bayyana mana cewa Kasashen Musulmi kadai ne keda damar tarayya a wasannin saboda ISSF din yayi, shine yasa muke neman bayanin shin Najeriya kasar Musulmi kadai ce ko ta kowa da kowa “Muna nema a bincika hakan don hakan ya sabawa kundin tsari na zamantakewar addinai yankin tsari na 10 daga kwanstitushan shekarar 1999 (gyararre).

Muna sake tunatar da najeriya cewa ita kasa ce ta kowa da kowa, sakamakon haka ya kamata a lura da hakkokin kowa ba tareda karkata zuwa ga bangare daya ba. Yin sabanin hakan kuwa na iya bayuwa zuwa ga tashin-tashina da rashin zama lafiya a kasa.''

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon zanga-zangar da akyiwa wani sanata a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel