Muna tare da mataimakin shugaban kasa Dari bisa Dari – Inji Dattawan Arewa

Muna tare da mataimakin shugaban kasa Dari bisa Dari – Inji Dattawan Arewa

- Kungiyar Dattawan Arewa NEF sun nuna goyon bayansu ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayinsa na shugaban Kasa na wucin gadi.

- Bayan haka kuma kungiyar ta jinjina wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari da irin namijin kokarin da yakeyi na ganin ya bi yadda dokar kasa ta shimfida musamman wajen mika mulki ga mataimakinsa idan zai bar kasa.

Mataimakin kungiyar Paul Unongo ne ya sanar da hakan da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da kungiyar tayi a Kano.

NAIJ.com ta samu labarin yayi kira ga mutanen kasa da su ba Osinbajo hadin kai domin samun nasara akan abinda ya sa a gaba.

Muna tare da mataimakin shugaban kasa Dari bisa Dari – Inji Dattawan Arewa

Muna tare da mataimakin shugaban kasa Dari bisa Dari – Inji Dattawan Arewa

KU KARANTA: Aisha Buhari tayiwa yan matan Chibok 19 ta arziki

Kungiyar ta yabi Buhari da irin kokarin da yayi wajen ganin an kusa kawo karshen babban matsalar da yankin Arewa take ta fama dashi wato matsalar Boko Haram. Sannan sun yaba wa shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da na Majalisar Dattawa Bukola Saraki kan irin nasu gudunmuwar da suke ba shugaban kasa.

Kungiyar tace yanzu haka tana zazzagayawa jihohin arewa ne domin ganin abubuwan da ke faruwa da kuma bada shawarwari akan abinda suka ga ya dace ayi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel