Zabukan 2019 za su fi na 2015 inganci - Inji Shugaban INEC

Zabukan 2019 za su fi na 2015 inganci - Inji Shugaban INEC

- Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar sa na bakin kokarin ta wajen tabbatar da cewa zabukan da za a gudanar nan gaba sun fi wanda aka gudanar a 2015 inganci.

- Yakubu ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ke karbar bakuncin Jakadan Amurka a Nijeriya, Stuart Symington a ofishin hukumar zabe, a Abuja. Ya kuma nuna godiyar sa ganin cewa Amurka ta nuna gamsuwar ta dangane yadda Nijeriya ta gudanar da zaben 2015.

NAIJ.com ta samu labarin a ta bakin sa, “Kun lura da cewa zaben 2015 ya tsaru sosai kuma an shirya shi a natse a cikin inganci. Sannan kuma ya yi daidai da dukkan ka’idojin zabe na kasa da kasa da aka amince da shi a duk diniya, sabanin zabukan can baya wadanda jama’a kan fito suna tayar da tarzoma kan tituna bayan gudanar da zaben.”

Shugaban na Hukumar Zabe ya kara da cewa hukumar sa za ta ci gaba da tantancewa da aikin bada rajistar zabe a dukkan fadin kananan hukumomi 774 na kasar nan kafin 2019.

Zabukan 2019 za su fi na 2015 inganci - Inji Shugaban INEC

Zabukan 2019 za su fi na 2015 inganci - Inji Shugaban INEC

KU KARANTA: Ra'ayoyin yan Najeriya game da tafiyar BUhari Landan

Tun da farko, a nasa jawabin, Symington ya bayyana cewa wannan ziyara da ya kai wa Hukumar Zabe, ya je ne domin sanin yadda Nijeriya ta gudanar da zaben ta. Ya kuma yaba wa hukumar a kan nasarar zaben 2015.

Jakadan ya kuma ce kusan ra’ayoyin jama’a a duniya ya fi karkata wajen jaddada cewa zaben 2015 da Nijeriya ta gudanar, ingantacce ne, kuma sahihi da aka gudanar a cikin yanayi na zaman lafiya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel