Yan Najeriya 193 ke mutuwa kowanne awanni 24 daga cutar daji – Masana

Yan Najeriya 193 ke mutuwa kowanne awanni 24 daga cutar daji – Masana

- Masana sun koka kan wanzuwar ciwon daji a tsakanin jama'an Najeriya

- Wani Farfesa ya bayyana cewar sama da mutane 100 ne ke mutuwa a duk rana sakamakon cutar

Ana samun mutum guda dan Najeriya dake mutuwa cikin minti bakwai daga cutar daji (Cancer), kwatankwacin mutane 193 kenan ke mutuwa a duk awa 24, kamar yadda wani Farfesa Sunday Ene-Ojo Atawodi ya bayyana.

Farfesa Atawodi malami a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ya bayyana haka ne a taron masana ilimin kimiyya daya gudana a garin Abuja inda ya bayyana cewar dalilin daya sa cutar daji ke hallaka yan Najeriya da dama shine sakamakon rashin kayan aiki da magunguna.

KU KARANTA: Hamid Ali yayi sabbin naɗe naɗen muƙamai a hukumar Kwastam

Farfesa Atawodi yace duk da cewa ana maganin cutar daji, amma yan Najeriya basa zuwa asibiti neman magani har sai ta cinye su, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Farfesan ya koka kan karancin wayewar kan al’umma dake tattare da cutar, inda ya bukaci yan majalisu suyi wata doka da zata taimaka wajen wayar da kan jama’a tare da samar da kulawar data dace gare su:

“Dama mu yan Najeriya bamu da kokarin magance cututtuka, kuma ga tsadar magance cutar daji a Najeriya, don haka ya dace gwamnati ta sawwaka kudin, tare da samar da isassun kayayyakin aiki don maganin cutar.”

Daga karshe majiyar NAIJ.com ta ruwaito Farfesan yan ja hankalin gwamnati inda yace:

“Kungiya kula da lafiya ta duniya ta bukaci a samar da na’urar maganin cutar daji guda 1 ga duk mjtane miliyan daya, kaga kenan muna bukatar guda 180 ga jama’an Najeriya miliyan 180. Amma abin kunya guda 8 kacal muke dasu a Najeriya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin yaushe ne za'a samu matashin shugaban kasa a Najeriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel