Ayarin motocin wani gwamna sunyi taho mu gama da motar babban bankin Najeriya (Hotuna)

Ayarin motocin wani gwamna sunyi taho mu gama da motar babban bankin Najeriya (Hotuna)

- Gwamnan Ibikunke Amosun ya sha da kyar biyo bayan hatsarin mota

- Hatsarin ya faru ne sakamakon taho mu gama da ayarin motar gwamnan tayi da motar dakon kudi

Gwamnan jihar Ogun sanata Ibikunle Amosun ya tsallake rijiya da baya a ranar Alhamis 11 ga watan Mayu sakamakon wani hadari daya ayku tsakanin ayarin motocinsa da motar babban bankin Najeriya dake dakon kudi.

Wannan hadari ya faru ne akan titin Legas zuwa Ibadan, a daidai kwanar Ibafo a lokacin da gwamnan ke kan hanyarsa ta zuwa jihar Legas don gudanar da wani aiki na musamman.

KU KARANTA: Hamid Ali yayi sabbin naɗe naɗen muƙamai a hukumar Kwastam

Wata sanarwa da NAIJ.com ta samu ta bakin Kaakakin gwamnan Adejuwon Soyinka, tace motar babban bankin na cikin matsanancin gudu ne a lokacin da tayi kokarin shan gaban ayarin motocin gwamnan ba tare da kulawa ba.

Ayarin motocin wani gwamna sunyi taho mu gama da motar babban bankin Najeriya (Hotuna)

Gwamna Amosun a inda hatsarin ya wakana

Duk da kokarin gargadin direban motar da jami’an tsaron gwamnan suka yi, sai daya afka ma motocin dake cikin ayarin gwwamnan, har da motar gwamnan.

Ayarin motocin wani gwamna sunyi taho mu gama da motar babban bankin Najeriya (Hotuna)

Gwamna Amosun yana duba motar banki

Dayake nuna bacin ransa dangane da hatsarin, gwamna Amosun yace:

“Wannan rashin bin dokar hanya ce, idan haka kai iya faruwa ga gwamna a jihar sa, me kenan zai faru ga sauran jama’a? don haka ba zamu bari hakan ya dinga faruwa a jihar Ogun ba.”

Ayarin motocin wani gwamna sunyi taho mu gama da motar babban bankin Najeriya (Hotuna)

Jami'an tsaro a wajen

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda gwamna ya nuna ma matarsa soyayya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel