Tattalin arziki: Naira ta doke Dala a kasuwa

Tattalin arziki: Naira ta doke Dala a kasuwa

– Dala ta dan sha kasa kadan a kasuwa

– Naira ta dan karfi yayin da CBN ke cigaba da kokari

– Dala ta tashi a kan N386 a jiya

Jiya NAIJ.com ta kawo maku rahoton cewa Naira ta ki girgiza a kasuwar canji

Yanzu ma dai abin ya fi da kyau don kuwa Naira ta kara daraja.

A jiya an saida Dala kan N386 a hannun ‘yan kasuwa.

Tattalin arziki: Naira ta doke Dala a kasuwa

Gwamnan CBN Na kasa

Babban bankin kasar na CBN na cigaba da sakin makudan daloli a kasuwa domin a samu saukin tashin Dalar Amurka. A jiya mu ka ji cewa bankin kasar ya saki sama da Dala Miliyan 80 masu tafiya asibiti ko zuwa karatu kasar waje.

KU KARANTA: Tattalin Najeriya zai kara bunkasa badi

Tattalin arziki: Naira ta doke Dala a kasuwa

Dala ta sha kashi a kasuwa

Haka kuma an saki wasu kudi ga kananan ‘yan kasuwa kamar yadda CBN din ta tabbatar da kan ta. Watakila wannan ne dalilin da ya sa Dalar ta rage daraja jiya inda ta tashi kan N386 a kasuwa yayin da ake saida ta N306 a banki.

Gwamnan CBN Godwin Emefiele yace su na kan hanyar gyara abubuwa a kasar kuma bugu-da-kari ma kwanan nan za a saki kasafin kudin bana. IMF mai bada lamuni ta Duniya kan ta tayi na’am da tsarin tattalin arzikin Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani Ministan Buhari yace bai son kudi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel