Yau tsohon ministan Abuja Bala Mohammad zai bayyana a kotu

Yau tsohon ministan Abuja Bala Mohammad zai bayyana a kotu

- Hukumar EFCC zai bayyana da tsohon ministan Abuja Bala Mohammad a wani kotu da ke birnin tarayya Abuja

- Hukumar na zargin ministan kan bayanai ba dai-dai ba kan gidaje

A yau Juma’a, 12 ga watan Mayu za a dawo da sauraron shari’ar tsohon ministan Abuja sanata Bala Mohammad, gaban kotun birnin tarayya wadda ta tura shi zaman wakafi a gidan yarin Kuje.

Hukumar yaki da almundahana ta gurfanar da ministan kan zargin bayanai ba dai-dai ba kan gidaje, da duk kuwa sabuwar tuhumar da ta kai caji shida ta kai darajar kudi naira miliyan 864.

Tuni lauyan sanata Bala, Chiris Uche, ya bukaci bada belin tsohon ministan, sakamakon beli da aka bashi kan tsohuwar tuhuma, Uche ya nuna gamsuwa ga abin da yace kotun ba ta kawo wasu lamura masu sarkakiya ba.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, lauyan EFCC, Ben Ikani, yaki amincewa da bada belin Bala, yana mai cewa hakan zai shafi aikin hukumar da doka ta daura mata. Ya ce akwi zargin bada shaida ta barauniyar hanya kan wani gida da darajarsa ma ta kai fiye da rabin naira Biliyan ‘daya.

KU KARANTA KUMA: Abin da Shugaba Buhari yayi kawo hadin kai ne ga gwamnatin kasa – Lauya

Mai shari’a zai duba yiwuwar bada beli kafin ci gaba da gudanar da shari’ar. Hukumar EFCC dai ta rike tsohon sanatan a lokuta mabanbanta, inda magoya bayansa kan yi tururuwa zuwa hedikwatar hukumar dan jajantawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jami'an sojoji ne suka sace hadimi na - Inji Sanata Shehu Sani

Jami'an sojoji ne suka sace hadimi na - Inji Sanata Shehu Sani

Jami'an sojoji ne suka sace hadimi na - Inji Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel