An koma Kotu da Ma’aikacin matar tsohon shugaban kasa Jonathan

An koma Kotu da Ma’aikacin matar tsohon shugaban kasa Jonathan

– Ana ta faman shari’a tsakanin EFCC da Emmanuel Dudafa

– Dudafa ne mai ba tsohon shugaban kasa shawara kan harkokin cikin gida

– Sai dai jiya lauyoyin EFCC ba su halarci shari’ar ba

Hukumar EFCC na zargin wani na-kusa da tsohon shugaban kasa Jonathan da sata.

Ana zargin sa da yin sama da Dala Miliyan 15.5.

Sai dai jiya an dage karar saboda wasu dalilai.

An koma Kotu da Ma’aikacin matar tsohon shugaban kasa Jonathan

Dudafa mai ba Jonathan shawara

Kamar yadda ku ka ji daga NAIJ.com Hukumar EFCC mai yaki da barna na zargin wani na-mai ba tsohon shugaban kasa Jonathan shawara da laifin satar wasu kudi masu dinbin yawa tare da wasu mutane 2.

KU KARANTA: Majalisa za ta gayyaci Magu da Emefiele

An koma Kotu da Ma’aikacin matar tsohon shugaban kasa Jonathan

Ma’aikatan Hukumar EFCC

EFCC na zargin Mista Emmanuel Dudafa da yin gaba da Dala Miliyan 15.5 da sunan wasu kamfani. Sai dai dole ta sa aka dage shari’ar har zuwa Watan Satumba bayan da Lauyoyin EFCC masu kara su ka gaza halartar kotun.

Idan kuna tare da NAIJ.com kwanakin baya ne dai Kotu ta kara bada umarni a daskare asusun matar tsohon shugaban kasar Patience Jonathan bayan an samu makudan daloli a ciki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Buhari ya bar Najeriya; Ka ji ra'ayoyin Jama'a

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha duka da cizo a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha duka da cizo a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha duka da cizo a hannun wata mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel