Aisha Buhari tayi ma yan matan Chibok su 82 da aka sako 19 na arziƙi (Hotuna)

Aisha Buhari tayi ma yan matan Chibok su 82 da aka sako 19 na arziƙi (Hotuna)

- Uwargidar shugaban kasa Aisha Buhari ta gana da yan matan Chibok da aka sako

- Aisha Buhari ta bi yan matan na Chibok da kyaututtuka da dama

Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta yi alkawarin sake tsugunar da yan matan Chibok din nan 82 da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta sako, kamar yadda NAIJ.com ta samo rahoto.

Aisha Buhari tayi wannan alkawari ne yayin da take ganawa da yan matan a fadar shugaban kasa a ranar Laraba 10 ga watan Mayu, inda ta shawarce su dasu mayar da hankali ga iliminsu da zarar an tsugunnar dasu.

KU KARANTA: ‘Ziyarar ban girma ce na kai ma muƙaddashin shugaban ƙasa’ – Namadi Sambo

Aisha ta samu rakiyar ministan watsa labaru Lai Muhammed, ministan al’amuran mata Jummai Alhassan, uwargidar mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo, tare da wasu daga cikin matan gwamnonin kasar nan.

Aisha Buhari tayi ma yan matan Chibok su 82 da aka sako 19 na arziƙi (Hotuna)

Aisha Buhari tare da yan matan Chibok

“A lokacin da basa nan, mun sha kuka, mun yi addu’a Allah ya bayyana su, yanzu kuwa nayi farin cikin dawowar ku, ina fatan sauran yan matan ma zasu dawo cikin koshin lafiya.” Inji Aisha.

Aisha Buhari tayi ma yan matan Chibok su 82 da aka sako 19 na arziƙi (Hotuna)

daya daga cikin yan matan Chibok

Da take jawabin a madadin yan matan na Chibok, Rhoda Chibok ta gode ma gwamnatin tarayya dangane da kokarin da tayi na ganin sun fito daga hannun yan ta’adda, sa’annan ta kara da rokon gwamanti ta taimaka ta kwato saura matan.

Ga sauran hotunan:

Aisha Buhari tayi ma yan matan Chibok su 82 da aka sako 19 na arziƙi (Hotuna)

Yan matan Chibok

Aisha Buhari tayi ma yan matan Chibok su 82 da aka sako 19 na arziƙi (Hotuna)

Aisha Buhari da yan matan Chibok

Aisha Buhari tayi ma yan matan Chibok su 82 da aka sako 19 na arziƙi (Hotuna)

Jerin yan matan Chibok

Aisha Buhari tayi ma yan matan Chibok su 82 da aka sako 19 na arziƙi (Hotuna)

Aisha Buhari da Dolapo Osinbajo tare da yan matan Chibok

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Iyayen yan matan Chibok sun koka

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel