Hamid Ali yayi sabbin naɗe naɗen muƙamai a hukumar Kwastam

Hamid Ali yayi sabbin naɗe naɗen muƙamai a hukumar Kwastam

- Anyi ma mukamai da dama a hukumar kwastam garambawul

- Shugaban hukumar ya bukaci wadanda sauyin ya shafa dasu dage wajen inganta ayyukan hukumar

Hukumar hana fasakauri ta kasa, wato Kwastam ta gudanar da aikin sauye sauye ga manyan jami’an ta inda ta canja musu mukamai domin inganta ayyukan hukumar.

Kaakakin hukumar Joseph Attah ne ya bada wannan sanarwar a ranar Laraba 10 ga watan Mayu kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

KU KARANTA: FIFA ta fara bin bahasin bahallatsar cinikayyar ɗan wasan Man-U, Pogba

Attah yace “Hukumar ta nada sabbin mataimakan shugaban hukumar guda hudu da kuma mataimakan shugaban hukuma a mataki na biyu har guda bakwai don karfafa ayyukan hukumar, sa’annan shugaban hukumar, Hamid Ali ya amince da canja ma wasu kwantrololi guda takwas wajen aiki.”

Hamid Ali yayi sabbin naɗe naɗen muƙamai a hukumar Kwastam

Jami'an hukumar Kwastam

Attah ya bayyana sunayen jami’an da sauyin ya shafa da suna Alu Robert, DCG mai kula da sanya kudi da cinikayya, Olubiyi Ronke, mai kula da dauka lamurran ma’aikata, sauran sun hada da mukaddashin DCG Dangaladima Aminu, mukaddashin DCG Iferi Patience sai mukaddashin DCG Chidi Augustine.

Attah ya cigaba da bayyana sauran kamar su ACG Hamza Ladan, ACG Ekekezie Kaycee, ACG Haruna Mahmoud, ACG Sarki Umar da ACG Enwereuzor Francis.

Haka zalika an kara ma Dahiru Aminu matsayi zuwa mukaddashin ACG mai kula da yankin Abuja, sai kuma Umar Abubakar da aka kara masa likafa zuwa mukaddashin ACG mai kula da sashin kudi, mulki da aikace aikace.

Kaakakin hukumar ya kara da cewa shugaban hukumar kwastama ya bukaci jami’an dasu zage damtse tare da yin amfani da kwarewarsa wajen ganin sun inganta aikin hukumar.

“Ya zama wajibi mu tabbata cewa nasarorin da muka samu mun daure da shi musamman a fannin samar da kudaden shiga da hana fasa kauri.” Inji Attah.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan Najeriya sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi game da tafiya Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel