Majalisa na neman Magu, Munguno da Gwamnan CBN

Majalisa na neman Magu, Munguno da Gwamnan CBN

– Majalisa za ta gurfanar da shugaban NIA da aka dakatar Oke

– EFCC ta bankado wasu makudan kudi a wani a Ikoyi

– ‘Yan Majalisar za su ji ta bakin NSA Babagana Munguno

Kwanaki aka gano sama da Naira Biliyan 15 a wani gida a Ikoyi.

Hukumar NIA dai tace wannan kudi na ta ne.

Tuni aka dakatar da shugaban aka shiga bincike.

Majalisa na neman Magu, Munguno da Gwamnan CBN

Shugaba Buhari ya dakatar da shugaban NIA

Muna jin labari daga Jaridar Daily Trust cewa shugaban Hukumar NIA da aka dakatar Ambasada Ayo Oke zai gurfana gaban Majalisa nan ba da jimawa ba. Wannann bai rasa alaka da kudin da aka gano kwanaki a Ikoyi.

KU KARANTA: An hana Andrew Yakubu Dalolin da aka samu a gidan sa

Majalisa na neman Magu, Munguno da Gwamnan CBN

Kudin Ikoyi: Majalisa na neman Munguno da Gwamnan CBN

Honarabul Aminu Sani wani Dan Majalisar APC na Jihar Zamfara shi ne shugaban kwamitin tsaron kasa ya kuma gayyaci mai ba shugaba Buhari shawara kan harkar tsaro Babagana Munguno da Gwamnan CBN da kuma Shugaban EFCC domin jin ta bakin su.

NAIJ.com na samun labari daga wurare dabam-dabam cewa akwai shirin tursasawa Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sauka daga kujerar sa kafin zaben 2019. Osinbajo ne dai yayi bincike game da kudin na Ikoyi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Anthony Oluwafemi Joshua ya zama dan damben Duniya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji a jihar Ondo

Rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji a jihar Ondo

Rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji a jihar Ondo
NAIJ.com
Mailfire view pixel