Shugaban cocin Anglican ta tarayya ya yabawa shugaba Buhari

Shugaban cocin Anglican ta tarayya ya yabawa shugaba Buhari

- Shugaban baban cocin Anglican na Zaria ya yaba wa shugabancin shugaban kasar Muhammadu Buhari

- Reverend Abiodun ya ce shirun shugaba Buhari a kan rikicin kudancin Kaduna ya na matsayin "kisan kare dangi" da kuma "mugunta”

Shugaban baban cocin Anglican na Zaria ya yaba wa kokarin da gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi kan yadda ya durkushe Boko Haram.

RT. Reverend Abiodun Ogunyemi ya bayyana haka, ya ce kasawar tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan wajen yakan Boko Haram ta yi sanadiyar mumunar barnar hare-haren ta’addanci a yankin arewa maso gabas.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya isa jihar Katsina

Yana ce: "Muna so mu yaba wa gwamnatin yanzu na shugaban kasar Muhammadu Buhari kan fatattakar 'ya'yan kungiyar Boko Haram daga yankin arewa maso gabas”.

A cewarsa: " Dole ne kuma mu yaba wa rundunar sojojin Najeriya kan sadaukar da rayuwarsu ga kasar Najeriya”.

Duk da haka, shugaban ya bayyana cewa shirun shugaba Buhari a kan rikicin kudancin Kaduna ya na matsayin "kisan kare dangi" da kuma "mugunta”.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shugaba Buhari rike da jaririyar yariyan Chibok da ta tsirar a hannun Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel