Abin da Shugaba Buhari yayi kawo hadin kai ne ga gwamnatin kasa – Lauya

Abin da Shugaba Buhari yayi kawo hadin kai ne ga gwamnatin kasa – Lauya

- Sanata Mao Ohuabunwa yayi maganar ne a majalisa sakamakon lura da yayi gameda yanayin lafazin shugaban gameda furta Osinbajo a mukaddasi

- Eletu, Lakcara a jami'ar legas ya nuna cewa bin sauye-sauyen rai bashida amfani tunda shugaban ya bayyana a wasikar dalilansa da ke kan ka'idar kasa

Wani Lawya Mai zaman kansa a Jihar Legas, Mr Shakiru Eletu, ya kwatanta Ja'inja dake gudanuwa gameda wasikar da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika zuwa ga majalisar zartarwa da cewa ba Abune mai amfani ba a yanzu.

Eletu, Lakcara a jami'ar legas ya nuna cewa bin sauye-sauyen rai bashida amfani tunda shugaban ya bayyana a wasikar dalilansa da ke kan ka'idar kasa

''Shugaban yayi abinda bai sabawa kundin tsari na kasa ba, ba sai ya furta cewa mataimakinsa ya zama mai rikon kwarya ba tunda akwai hakan a cikin kundin tsari.''

Ya nuna a cewar NAIJ.com cewa abinda Shugaban yayi kawai kokarin tabbatar da su ne akan hada kai ayi aiki tare, daura nauyin jibintar lamarin kasa a wuyan mataimakinsa bashida amfani a rubuce saboda akwai hakan a tsare-tsaren kundin kasar, kuma yin hakan ba abune da za'a jajirce akan yiwuwarsa ba ko rashin yiwuwa ba.

KU KARANTA: Gwamnati ta hana ni ganin sarakunan gargajiya – Yakubu Dogara

Lauyan ya nuna dan majalisar zartarwar na iya yin hakan da kyakyawar manufa ba don tada rigima ba.

“Sanata Mao Ohuabunwa na iya yin hakan don manufa mai kyau , sakamakon kyakyawar fahimtarsa wa dokokin kasa. Amma a zahiri babu wani abin kushe a wasikar ta shugaban kasar

“A mahangata, alakar dake tsakanin Shugaban da mataimakinsa alaka ce mai kyau kuma tana daf da kaiwa ga gaci, kuma ina kira ga yan siyasa da kada su ribaci wannan don tada zaune tsaye wa mulkin da ke gudanuwa.''

NAIJ.com ta tabbatarda cewa Sanata Mao Ohuabunwa ya daukaka maganar ne sakamakon lura da yayi gameda yanayin lafazin shugaban gameda furta Osinbaji Mukaddasi, kuma Sanata Saraki ya nuna kuskuren hakan.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel