FIFA ta fara bin bahasin bahallatsar cinikayyar ɗan wasan Man-U, Pogba

FIFA ta fara bin bahasin bahallatsar cinikayyar ɗan wasan Man-U, Pogba

- Hukumar kula da kwallon kafa ta fara bincikar sarkakiyar dake tattare da cinikin Paul Pogba

- FIFA ta bukaci kungiyar kwallon kafa ta Manchester data bata gamsassun bayanai dangane da cinikin

Hukumar kwallon kafa ta duniya, wato FIFA za ta binciki ciniki mafi tsada a duniya da Manchester United ta yi da Juventus, a kan sayen dan wasan tsakiya na kungiyar Paul Pogba, a shekarar da ta gabata.

FIFA ta rubuta wa kungiyar takarda tana neman Man U din ta yi mata cikakken bayani game da yarjejeniyar cinikin dan wasan, inji rahoton BBC Hausa.

KU KARANTA: Abin Al’ajabi: Gawa tayi tirjiya, ta nuna gidan wanda ya kashe ta (Hotuna da Bidiyo)

Ana so ne dai a gano su waye ke da hannu a cinikin da ya kai na fam miliyan 89.3, kuma ta ya ya aka biya su kudin.

FIFA ta fara bin bahasin bahallatsar cinikayyar ɗan wasan Man-U, Pogba

Pogba

Mai magana da yawun Man U ya ce, "Baya ma magana a kan kwantiragin mutum daya. Ya kara da cewa hukumar na da bayanai game da cinikin tun lokacin da aka yi shi a watan Agusta."

Pogba, mai shekara 24, ya kara dawo wa Old Trafford ne, bayan da ya bar ta ya koma Juventus kan kudi fam miliyan 1.5 a shekarar 2012, kamar yadda NAIJ.com ta gano.

Dan wasan tsakiyar na Faransa, ya fara zuwa United ne daga kungiyar Le Havre ta Faransa a shekarar 2009.

Ya kara dawo wa United a kakar wasa ta bara a matsayin dan wasa mafi tsada a duniya a kan kudi fam miliyan 105.

Haka kuma United din ta amince ta biya Juventus karin kudi fam miliyan 4.5 idan dan wasan ya kara sanya hannu da kungiyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli shirin da Super Eagles ke yi na shiga gasar cin kofin Duniya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel