Muhimman nasarori 5 da gwamnatin shugaba Buhari ta yi a jihar Borno

Muhimman nasarori 5 da gwamnatin shugaba Buhari ta yi a jihar Borno

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kokari ganin zaman lafiyar ta dawo yankin arewa maso gabas

- Shugaba Buhari ya cika daya daga alkawarin cewa zai kubutar da ‘yan matan Chibok daga hannun Boko Haram

Tabbas gwamnatin shugaba Buhari ta yi namijin kokari wajen kawo karshen haren-haren 'ya'yan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeria.

NAIJ.com ta tattaro wasu daga cikin nasarorin shugaban kasa Muhammadu Buhari a nan kasa:

1. Bayan shafe sama da shekaru biyu ba tare da bude makarantu ba sakamakon tsanantar hare-haren 'ya'yan kungiyar Boko Haram, cikin ikon Allah gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kawo karshen wannan matsala ta hanyar bawa harkar tsaro kyakkyawar kulawa, wanda hakan ya sa aka samu saukin hare-haren har ta kai ga an sake bude makarantu a ranar 26 ga watan Satumbar 2016.

2. Zaratan sojojin Nijeriya sun fatattaki ayarin mayakan Boko Haram daga matsugunnan su dake dajin Sambisa, inda hakan ya ba su damar kutsawa zuwa babbar Hedikwatar kungiyar ta Boko Haram kuma suka kwace madafun ikon hedikwatar daga hannun kungiyar ta Boko Haram a ranar Juma'a 23 ga watan Disambar 2016.

3. 'Yan matan Chibok sun shafe sama da shekaru 3 a hannun 'ya'yan kungiyar Boko Haram ba tare da gwamnatin wancan lokaci tayi wani yunkuri na azo agani ba wajen kubutar da rayuwarsu, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sha alwashin kubutarda wadannan 'yan mata tun a lokacin yakin neman zabe. A ranar Alhamis 13 ga watan Satumbar 2016 an samu nasarar kubutar da rukunin farko na 'yan mata 21 daga hannun 'ya'yan kungiyar ta Boko haram wanda yanzu haka 'yan matan suna karkashin kulawar gwamnatin tarayya.

4. Rukuni na biyu na 'yan matan Chibok mai dauke da mata 82 sun sami 'yanci a ranar 7 ga watan Mayu 2017

KU KARANTA KUMA: An gano makarkashiyar da ake kullawa a majalisar dattijai don tsige Buhari

5. Filin tashi da saukar jiragen sama na Maiduguri ya dawo aiki a ranar 9 ga watan Mayu na 2017 bayan da aka shafe tsawon shekaru 3 yana rufe saboda rikicin Boko Haram.

6. Kafun Allah ya kawo gwamnatin shugaba Buhari, hare-haren Boko Haram ya tursasa rufe wasu manyan hanyoyin sufuri wadanda suka hada jihar Borno da wasu sassan kasar nan. Bayan shafe tsawon shekaru 3 hanyoyin suna rufe, a ranar 26 ga watan Disambar 2016 hukumomin tsaro sun bude hanyoyin Maiduguri zuwa Gubio da kuma Maiduguri zuwa Monguno bayan fatattakar 'ya'yan kungiyar Boko Haram daga yankunan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayoyin mutane kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel