‘Ziyarar ban girma ce na kai ma muƙaddashin shugaban ƙasa’ – Namadi Sambo

‘Ziyarar ban girma ce na kai ma muƙaddashin shugaban ƙasa’ – Namadi Sambo

- A ranar Laraba ne tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya kai ziyara ga Farfesa Yemi Osinbaj

- Namadi ya samu tarba mai kyau daga mukaddashin shugaban kasa Osibanjo

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya sanarwa manema labarai cewa ya kawo wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ziyara ta musamman ne a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa sannan kuma domin ya sada zumunta. Inji rahoton Premium Times.

“ Kamar yadda kuka sani ne cewa tsofaffin shugabannin kasa sukan kawo wa shugaban kasa ziyara haka nima naga ya dace in kawo irin wannan ziyara wa mataimakin shugaban kasa.

KU KARANTA: Zaɓen ƙananan hukumomi: ‘Ƙwalelen PDP” – Inji Tinubu

“Don haka ne na kawo ziyarar don kara dankon zumunta, nayi farin cikin ganin ku, abokan aikina, kuma ina godiya da irin tarbar da kuka yi min.” Inji Namadi Sambo.

‘Ziyarar ban girma ce na kai ma muƙaddashin shugaban ƙasa’ – Namadi Sambo

Osinabjo da Namadi Sambo

Namadi Sambo ya kai ma Osinabjo ziyara ne a ranar Laraba 10 ga watan Mayu bayan kwanaki uku da tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa kasar Landan, tare da mika ragamar mulkin kasa a hannun sa.

Majiyar NAIJ.com tace da aka titsiye shi akan yayi bayanin mai suka tattauna, tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo yace ba zai bayyana wannan ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hotunan takarar shugaba Buhari sun watsu a birane

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel