Jami'an hukumar NDLEA sun yi babban kamu a arewa

Jami'an hukumar NDLEA sun yi babban kamu a arewa

- Jami’an hukumar kula da safara da fasakaurin miyagun kwayoyi na reshen jihar Gombe NDLEA sun kama wasu makiyaya biyu dauke da bindiga da wasu miyagun kwayoyi masu bugarwa.

- Kwamandan hukumar Aliyu Adole ne ya sanar da hakan wa manema labarai a garin Gombe.

Aliyu yace sun yi garkuwa da Mijinyawa Shehu dan shekara 30 da bindiga kirar ”Jericho pistol” tare da shi kuma kaninsa mai suna Abdul Shehu mai shekara 25 da suke tare dauke da wasu kwayoyin da ya kai gram 300 a kauyen Wangi-Zange, karamar hukumar Dukku.

NAIJ.com ta samu labarin cewa bayan haka Adole yace ma’aikatansa sun gano harsashen bindigar boye a wajen kwanan makiyayan.

Jami'an hukumar NDLEA sun yi babban kamu a arewa

Jami'an hukumar NDLEA sun yi babban kamu a arewa

KU KARANTA: Naira ta hana Dala sakat a kasuwannin canji

Da a ke tuhumarsa akan mallakar wannan bindiga, yace bindgan ta yi shekara biyu a hannunsa sai dai babu wani cikin ‘yan uwansa daya san cewa yana ajiye da bindigan.

Hukumar NDLEA ta ce ta danka Mijinyawa ga ‘yan sanda domin ci gaba da yin bincike akansa sannan shi kuma Abdul za su kai shi kara a babbar kotun kara domin muamula da kwayoyin da yak e yi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel