Tambuwal: Jihar Sakkwato ta samarda ayyuka 27,166 a bangaren noma

Tambuwal: Jihar Sakkwato ta samarda ayyuka 27,166 a bangaren noma

- Gwamnatin jihar sakwato ta fadi cewa ta samar da ayyukan 27,166 a tsawon shekaru biyu

- Gwamnatin kasa tareda hadin guiwar IFAD na samarda tarurrukan ilimi da ilmantarwa musamman gameda canjin yanayi don kyautatuwar harkar noma a fadin Najeriya

Gwamna Aminu Tambuwal yaci maganar ne a Larabar jiya a wani taron kararawa ilimi na canjin yanayi da alakarsa da tallafin harkokin noma.

Ya ce: ''A kokarin sauke hakkin da ke kanmu, mun taimakawa mutane sama da 33,000, a cigaban tarda ingantarcen noma da ayyukan da keda alaqa dashi, mun samarda asibitocin kulada lafiyar daabbobi, da samarwa matan manoma aikin yi.

“Daura da hakan mun samar da ayyuka masu alaka da aikin gona a hukumomin jihar guda 27,166 wa mazauna birane da kauyuka.”

KU KARANTA: Osinbajo zai kaddamar da wata asibiti a Katsina a yau Alhamis

Gwamnan ya tabbatar a daga labaran NAIJ.com cewa gwamnatinsa a shirye take don yawaita abinci da cigaba da kawo amfani da farinciki wa masu sana'ar noma a jihar musamman matasa.

Zamu cigaba da girmamawa tareda cika alkawurra da hada guiwa da kungiyar IFAD da sauran jam'iyyoyin tallafi don kyautatuwar mutanen mu."

A sakon fatan alkhairi Ministan harkokin noma da ci gaban karkara, Audu Ogbeh, da ya wakilci daraktan Arewa maso yammacin kasa , Adeyemi Ayoyeyi, "yace Gwamnati a shirye take don tabbatarda cigaban harkokin noma a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

“Gwamnati na tsara shirye-shiryen tabbatar da matasa akan samun aikin yi da shiga harkar noma da ganin darajarta.

Gwamnatin kasa tareda hadin guiwar IFAD na samarda tarurrukan ilimi da ilmantarwa musamman gameda canjin yanayi don kyautatuwar harkar noma a fadin Najeriya.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon game da Shugaba Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel