Kotu ta bada umurnin a kashe wani matashi da ya kashe uban sa sabo gado

Kotu ta bada umurnin a kashe wani matashi da ya kashe uban sa sabo gado

- Wata Babbar kotu dake babban birnin jihar Ekiti, Ado Ekiti, ta yankewa wani matashi mai suna Blessing Olumakinde Egunlae, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da ta same shi da laifin kisan mahaifinsa.

- Babban alkalin jihar mai Shari’a Ayodeji Daramola,wanda ya zartar da hukuncin a jiya talata,yace hujjojin da suke gaban kotu sun tabbatar da cewa ,mutumin da ake zargi ya aikata kisan kai.

NAIJ.com ta samu labarin yace masu gabatar da kara sun tabbatar da kwararan hujjojin dake nuni da cewa mutumin lallai ya aikata laifin, saboda haka na yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An dai gurfanar da Olumakinde, ne bisa tuhumar kisan mahaifinsa mai mata 6 da kuma yaya 18.

Iyalin marigayin sun dade suna samun sabani kan rabon gonar da marigayi Egunlae ya mallaka.

Kotu ta bada umurnin a kashe wani matashi da ya kashe uban sa sabo gado

Kotu ta bada umurnin a kashe wani matashi da ya kashe uban sa sabo gado

KU KARANTA: Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi ya yi bayani

Bayan da bai gamsu da yadda mahaifin nasa yayi rabon ba, Olumakinde dan shekara 47, yabi sahun mahaifinsa zuwa gona, inda ya sassara shi da adda.

Wata shida akayi ana nemansa kafin daga bisani ya mika kansa wurin yan sanda.

A bayanan da yayi wa yan sanda mutumin da ake zargi yace ya kashe mahaifinsa ne a cikin wani dakin Bukka dake cikin gonar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad
NAIJ.com
Mailfire view pixel