Rikita-Rikita: An gano makarkashiyar da ake kullawa a majalisar dattijai don tsige Buhari

Rikita-Rikita: An gano makarkashiyar da ake kullawa a majalisar dattijai don tsige Buhari

- Wata kungiyar matasa a karkashin Jam’iyyar APC ta ce ta gano wata makarkashiya da wasu sanatoci da manyan ‘yan siyasar kasar ne ke shirya wa da nufin cilla kasar cikin rikici, da sunan lafiyar Buhari.

- A wata sanarwa da sakataran kungiyar, Collins Edwin ya fitar a jiya Talata, ya bayana cewa Buhari bai saba wata doka ba da ya fada wa ‘Yan Nijeriya gaskiyar halin da yake ciki.

Ya ce akwai wasu mutane da ke yunkurin amfani da sashe na 144 na kundin tsarin mulkin kasa wajen tabbatar da Buhari a matsayin wanda ya gaza kuma ba zai iya ci gaba da rike mukamin shugabancin kasar ba.

Rikita-Rikita: An gano makarkashiyar da ake kullawa a majalisar dattijai don tsige Buhari

Rikita-Rikita: An gano makarkashiyar da ake kullawa a majalisar dattijai don tsige Buhari

KU KARANTA: Za'a ga watan Ramadana a 26 ga watan Afrilu

NAIJ.com ta samu labarin a kan haka ne kungiyar ta ja kunnen ‘yan siyasan da ke da wannan nufi da su shiga hankalin su su sauya tunani ko kuma su fuskanci bacin rai.

Sun kuma yi kira ga jami’an tsaro da su dauki mataki wajen magance illolin yawan maganganu barkatai da mutane ke yi, musammam ma a wannan lokaci da zaben 2019 ya ke karato wa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel