Zaɓen ƙananan hukumomi: ‘Ƙwalelen PDP” – Inji Tinubu

Zaɓen ƙananan hukumomi: ‘Ƙwalelen PDP” – Inji Tinubu

- Gwamnatin jihar Legas ta fara shiryeshiryen gudanar da zabukan kananan hukumomi

- Jigon jam'iyyar APC, Ahmed Tinubu yace ba zasu bari jam'iyyar adawa ta PDP ta lashe ku kujera daya ba

Jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu yace bai gat a yadda jam’iyyar PDP zata lashe koda kujerar Kansila a zabukan kananan hukumomin jihar Legas dake karatowa.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Laraba 10 ga watan Mayu yayin taron jam’iyyar reshen jihar Legas daya gudana a babban ofishin jam’iyyar don shirya ma zabukan dake tafe a ranar 22 ga watan Yulio.

KU KARANTA: Anyi aringizon kasafin kuɗin bana da naira miliyan dubu 149 a majalisa

Tinubu ya nuna bacin ransa na yadda APC tayi asarar wasu kujerun yan majalisun tarayya dana jiha, inda yace “Mun fafata a zabukan 2015, a zaben daya gabata mun yi asarar kananan hukumomi guda 3, don haka dole ne mu tambayi shuwagabannin mu a wadannan kananan hukumomi damu gano bakin zaren, don ganin APC sun kwato kujerun.”

Zaɓen ƙananan hukumomi: ‘Ƙwalelen PDP” – Inji Tinubu

Tinubu da gwamna Ambode yayin taron

NAIJ.com ta ruwaito Tinubu yana yaba ma jama’a jihar Legas sakamakon goyon bayan da suke baiwa gwamnatin gwamna Ambode.

“Gwamna Ambode bai bamu kunya ba, kuma yana kokarin duk da matsin tattalin arziki, ina alfahari da shi.”

Tinubu ya gargadi shuwagabannin jam’iyyar dasu guji cin hanci rashawa, inda ya shaida musu dalilin dayasa suka zabi ma’aikatan kananan hukumomi a matsayin shuwagabannin rikon kananan hukumomi.

Zaɓen ƙananan hukumomi: ‘Ƙwalelen PDP” – Inji Tinubu

Tinubu da Ambode a taron

Tinubu yace sun yi hakan ne domin baiwa yan siyasa daman tsayawa takara, tun da dais u ma’aikatan dake rike da kujerun a yanzu ba zasu yi takara ba.

Daga karshe Jigon APC ya shawarci shugabannin jam’iyyar a jihar data baiwa matasa da mata fifiko a kujerun takarar shugabancin kananan hukumomin jihar guda 57.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Legas, Ambode ya bukaci duk masu ruwa da tsaki dasu jajirce wajen ganin APC ta lashe dukkanin zabukan jihar Legas.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nayi da na sanin zaben APC, inji wani da APC

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel