Toh fa: ‘Yan Najeriya sun bukaci a fitar da rahoton binciken Babachir

Toh fa: ‘Yan Najeriya sun bukaci a fitar da rahoton binciken Babachir

- ‘Yan Najeriya sun bukaci mukaddashin shugaban kasa da ya gaggauta fitar da rahoton binciken Babachir

- Rashin gabatar da rahoton zai iya sanya shakku a zukatan al'umma game da yaki da cin hanci da rashawa

- Kwamitin binciken ta yi alkawarin mika rahoton sa a ranar 8 ga watan Mayu

A Najeriya, wasu masu fafutukar yaki da cin hanci a kasar sun bukaci mukaddashin shugaban kasa da ya gaggauta fitar da rahoton da ya bincike Babachir David Lawal, sakataren gwamnatin da aka dakatar bisa zargin aikata almundahana.

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al'umma ta CITAD da ke arewa maso gabashin Najeriya na daya daga cikin kungiyoyin da suka fara irin wannan kiraye kiraye.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, shugaban cibiyar Comrade Kabiru Sa'idu Dakata ya ce 'yan Najeriya sun zura ido suga an fitar da sakamakon binciken inda ya ce Jama'a da dama musamman masu fafutukar yaki da cin hanci a kasar na ganin beken gwamnatin saboda kin mika rahoton.

A cewar su, rashin gabatar da rahoton ka iya sanya shakku a zukatan al'umma game da yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin kasar.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na kai ziyara ga Osinbajo – Namadi Sambo

Tun da farko dai an tsara cewa kwamitin zai mika rahoton sa ne ranar 3 ga watan Mayu, amma kuma aka dage zuwa ranar Litini 8 ga watan Mayu wanda kuma ba'a gabatar ba.

Kwamitin binciken da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa dai ya hada da Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da kuma babban lauyan Najeriya, Abubakar Malami.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel