Sai da nayi kuka saboda yan matan Chibok su dawo – Aisha Buhari

Sai da nayi kuka saboda yan matan Chibok su dawo – Aisha Buhari

- Aisha Buhari tayi bayanin yadda tayi rayuwa kafin a sako yan matan Chibok

- Uwargidan shugaban kasa ta hadu da yan matan 82 da Boko Haram suka saki

- Kana kuma ta basu shawaran cewa su manta da abinda ya faru kuma su dogara da kansu

A ranan Laraba, 10 ga watan Mayu, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta yi alkwarin cewa zata taimakawa yan matan Chibok din da aka sako. Aisha Buhari ta basu shawaran cewa su manta da abinda ya faru, su koyi aikin hannu kuma su dogara da kansu.

Ta hadu da yaran a Abuja, tare da ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammadu, da ministan harkokin mata, Jummai Alhassan.

Sauran sune uwargidar mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo, Hajo Sani da kuma sauran matan gwamnoni.

Sai da nayi kuka saboda yan matan Chibok su dawo – Aisha Buhari

Sai da nayi kuka saboda yan matan Chibok su dawo – Aisha Buhari

Yayinda take magana da yaran, tace musu iliminsu nada matukar muhimmanci. “ Lokacin da aka sace ku, munyi hawaye kuma munyi addu’a da iyayenku domin dawowanku.

KU KARANTA: Naira ta kara daraja a kasuwan canji

Ina farin cikin cewa bayan shekarun kuka, sa rai, da addu’a, 82 daga cikin yan matanmu sun tsira.”

Har yanzu ina sa ran sauran yan matan zasu dawo cikin koshin lafiya,”.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel