Yau Majalisa za ta mika kasafin kudin bana

Yau Majalisa za ta mika kasafin kudin bana

– Yau ake sa ran Majalisa ta mika kasafin kudi bana

– Ana sa rai zartarwa ta rattaba hannu kan kasafin

– Lokaci dai yana nema ya kure

Tun kwanaki Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da cewa ana daf da kammala aikin kasafin kudi.

Sai wannan makon ne Sanatta Danjuma Goje ya kawo takardun.

A yau Alhamis ake sa rai cewa Majalisa za ta kammala komai.

Yau Majalisa za ta mika kasafin kudin bana

Shugaba Buhari wajen gabatar da kasafin kudi a Majalisa

A Ranar Alhamis Majalisa za ta mika kasafin kudin bana kamar yadda tayi alkawari. Har dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar kasar Majalisar ba ta kammala aiki ba duk da cewa an kai mata kudirin kasafin Tun karshen 2016.

KU KARANTA: Osinbajo ya gana da wani tsohon mataimakin shugaban kasa

Yau Majalisa za ta mika kasafin kudin bana

Majalisa za ta mika rahoton kasafin kudi

NAIJ.com ta samu labari cewa Majalisar ta kara kudin da ke cikin kasafin da kusan Naira Biliyan 150. Ita kan ta Majalisar akwai kishin-kishin din cewa ta kara yawan kasafin ta da tace za ta bayyana kowa ya gani wannan karo.

A bara ma dai sai da aka dauki dogon lokaci kafin a sa hannu a kasafin kudin bayan badakalar da ta shiga cikin aikin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana nema a kora wani Sanata gida

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad
NAIJ.com
Mailfire view pixel