Wasu daga cikin rukunin gidajen alfarmar gwamnati na kwantai a Kano

Wasu daga cikin rukunin gidajen alfarmar gwamnati na kwantai a Kano

- Wasu gidajen da gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso ta gina har yanzu mutane ba su shiga rukunin gidajen ba

- Gwamnati mai ci yanzu ta koka rashin sayar da gidajen saboda kukan cewa sun yi matukar tsada

- Wasu masana a jihar sun shawarci gwamnati cewa ta bada hayan gidajen da ba'a sayar ba

A Najeriya, yayin da kananan ma`aikata da sauran masu karamin karfi ke neman hanyar mallakar muhalli ido-rufe, wasu gidajen da gwamnati jihar Kano ta gina sun kama hanyar yin kwantai.

Har yanzu dai mutane ba su shiga rukunin gidajen Kwankwasiyya City da Amana City da kuma Bandirawo City ba, wadanda gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso ta gina.

Wani mai karamin karfi a jihar ya ce abin taikaci ne idan ya ga gidajen babu kowa a ciki. Ya ce: “Babu yadda za'a yi mai karamin ƙarfi ya mallaki gida na miliyan 27”.

Wasu daga cikin rukunin gidajen alfarmar gwamnati na kwantai a Kano

Wasu daga cikin rukunin gidajen alfarmar gwamnatin Rabiu Kwankwaso a Kano

KU KARANTA KUMA: Osinbajo zai kaddamar da wata asibiti a Katsina a yau Alhamis

Gwamnatin Ganduje dai ta ce ta gagara sayar da gidajen ne saboda masu karamin karfi na kukan cewa sun yi matukar tsada.

Ya kara da cewa tuni da dukufa wajen gina wasu sabbin gidaje masu daki uku-uku da ake sayar da su akan Naira miliyan 2 da 850,000 wadanda masu ƙaramin ƙarfin zasu iya saye.

Sai dai wasu masana sun ce kamata ya yi a bada hayan gidajen da ba'a sayar ba kasancewar sun yi tsada ga masu son saye.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon farashin kayayyaki a kasuwanni

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel