Majalisar dokokin jihar Kano za ta bincike sarkin Kano da masarautarsa

Majalisar dokokin jihar Kano za ta bincike sarkin Kano da masarautarsa

- Majalisar dokokin jihar Kano za ta bincike mai martaba sarkin Kano da majalisar masararutar Kano kan zargin kashe kudade ba tare da amincewar majalisar ba

- Majalisar na tuhumar sarkin Kano da aikata ba dai-dai ba akan abubuwa guda 8

- Majalisar ta baiwa kwamitin makonni biyu domin ta kammala bincikensa kuma ta gabatar da rahoto

Majalisar dokoki ta jihar Kano ta kafa kwaitin bincike akan mai martaba sarkin Kano da majalisar masararutar Kano, game da zargin kashe kudade ba tare da amincewar ita majalisar ba.

A zaman da majalisar ta yi a ranar Laraba, 10 ga watan Mayu karkashin jagorancin shugabanta Kabiru Alasan Rurum. ‘Yan majalisar sun yi muhawara akan kudurin da aka gabatar game da batun bincikar mai martaba sarkin Kano da masarautarsa.

Majalisar dai na tuhumar mai martaba sarkin Kano, Mallam Mohammadu Sanusi II, da aikata ba dai-dai ba akan abubuwa guda 8. A cewar ‘dan Majalisa Ibrahim Ahmed Gama, akwai korafi game da yadda sarki ke tsoma kansa cikin harkokin siyasa, sai kuma bayanai da aka samu kan yadda masarautar ta sarrafa makudan kudade ba bisa ka’ida ba.

Majalisar dokokin jihar Kano za ta binciki Sarkin Kano da masarautarsa

Mai martaba sarkin Kano, Mallam Mohammadu Sanusi II

Dokar da ta kafa masarautar Kano ta bayyana cewa masarauta ba zata kashe sisin kwabo ba, har sai ta kaiwa majalisar dokokin jihar Kano ta duba ta amince. Sai dai Ibrahim Gama, ya ce tun hawan mai martaba sarkin Kano bai taba kaiwa majalisar ba domin a amince masa kashe kudade.

Wannan kwamiti dai da majalisar ta baiwa makonni biyu domin ya kammala bincikensa kuma ya gabatar da rahoto, yana karkashin jagorancin mai tsawatarwa ne a zauren majalisar, Labaran Abdul.

KU KARANTA KUMA: Karya Faruk Lawan keyi akan batun kudin cin hanci na lokacin cire tallafin mai - Dan majalisa

Daya daga cikin ‘yan kwamitin Baffa Babba ‘Dan Agundi, ya ce zasu gayyato wanda ya mika korafin domin kara bayani gaban kwamitin, haka kuma za a gayyato mai martaba sarkin Kano da duk wadanda abin ya shafa domin su bada na su bahasin.

Wannan batu dai na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, ta kaddamar da na ta binciken akan mai martaba sarki da majalisar masarautarsa game da wannan batu na kashe kimanin Naira Biliyan 6 cikin shekaru 3 da suka gabata ba bisa ka’ida ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon da mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel