Osinbajo zai kaddamar da wata asibiti a Katsina a yau Alhamis

Osinbajo zai kaddamar da wata asibiti a Katsina a yau Alhamis

- Mukaddashin shugaban kasa zai ziyarci jihar Katsina don kaddamar da asibitin matsakaita da kananan masana'antu

- Osinbajo zai gana tare da 'yan kasuwa a kan kalubale da suke fuskanta

- Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta kafa wani kwamiti don wayar da kan 'yan kasuwa a kan muhimmancin ziyarar mukaddashin shugaban kasar

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai kaddamar da asibitin matsakaita da kananan masana'antu (MSMEs) a ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu a Katsina, wata bangare na yunkurin bunkasa tattalin arziki da ayyuka a kasar.

Kwamishinan ciniki, masana'antu da yawon shakatawa, Alhaji Abubakar Yusuf, ya sanar da wannan lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Katsina a ranar Laraba, 10 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya dauki matakin farko bayan tafiyar Buhari

Kwamishinan ya ce a lokacin ziyarar, Osinbajo zai gana tare da 'yan kasuwa a kan kalubale da suke fuskanta da kuma yadda za a shawo kan matsalolin.

Osinbajo zai kaddamar da wata asibiti a Katsina a yau Alhamis

Shugaba Buhari na ganawa da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo kafin tafiyarsa zuwa Landan

Yusuf ya ce gwamnatin jihar ta riga ta kafa wani kwamiti don wayar da kan 'yan kasuwa a kan muhimmancin ziyarar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayoyin mutane kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel