Gwamnan jihar Borno, sanata Ali Ndume da dattawan garin Chibok sun ziyarci ‘yan matan Chibok 82 (Hotuna)

Gwamnan jihar Borno, sanata Ali Ndume da dattawan garin Chibok sun ziyarci ‘yan matan Chibok 82 (Hotuna)

- Tawagar gwamnan jihar Borno sun ziyarci ‘yan matan Chibok 82 a birnin tarayya da ke Abuja

- Nana Shettima ta yiwa ‘yan matan kyautar akwati da tufafi a matsayin wani bangare na bayar da gudumawar su

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a ranar Talata, 9 ga watan Mayu ya jagoranci jami’in gwamnati da kuma dattawa daga garin Chibok zuwa ganin ‘yan matan makarantar Chibok 82 da aka kubutar daga hannun Boko Haram wadanda aka sace shekaru uku da ta wuje.

Tawagar gwamnan ya hada dattawa da Wakilin garin Chibok, sanata Mohammed Ali Ndume wanda ya wakilci Borno ta Kudu, 'yan majalisar wakilai da kuma ‘yan majalisar jihar Borno masu wakiltar Chibok da kuma sauran jami'an gwamnati daga Chibok.

Ministan harkokin Mata, Misis Jummai Alhassan ta bayyana cewa ko da yake 'yan mata 21 da aka sake a watan Oktoba, a bara, sun kasance a karkashin hannun gwamnatin tarayya inda gwamna Kashim Shettima ke bada gudunmawar kudi ga ma'aikatar na harkokin mata don kula da kuma koyawa ‘yan matan sanahohi daban-daban.

Gwamnan jihar Borno, sanata Ali Ndume da dattawan garin Chibok sun ziyarci ‘yan matan Chibok 82 (Hotuna)

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, sanata Ali Ndume da ministan harkokin mata, Misis Jummai Alhassan

KU KARANTA KUMA: Kotu ta umarci a ɗaure mata tsohon minista Bala Muhammed a gidan yari

NAIJ.com ta ruwaito cewa gwamna Shettima ya shaida wa 'yan mata da cewa yana cike da farin ciki kuma yana fatar samun sauran takwarorinsu nan bada jumawa ba.

Gwamnan jihar Borno, sanata Ali Ndume da dattawan garin Chibok sun ziyarci ‘yan matan Chibok 82 (Hotuna)

Baban darektan na asibitin DSS Medical Centre Misis Ann Okorafor a lokacin da take jawabi

Uwargidan gwamnan, Nana Shettima ta yiwa ‘yan matan 82 kyautar akwati da tufafi a matsayin wani bangare na bayar da gudumawar su.

Gwamnan jihar Borno, sanata Ali Ndume da dattawan garin Chibok sun ziyarci ‘yan matan Chibok 82 (Hotuna)

Tawagar gwamnan jihar Borno da ‘yan matan Chibok 82

Gwamnan jihar Borno, sanata Ali Ndume da dattawan garin Chibok sun ziyarci ‘yan matan Chibok 82 (Hotuna)

Akwati, kayan masarufi da tufafin da uwargidan gwamnan jihar Borno, Nana Shettima ta yiwa 'yan matan chibok 82

Gwamnan jihar Borno, sanata Ali Ndume da dattawan garin Chibok sun ziyarci ‘yan matan Chibok 82 (Hotuna)

Uwargidan gwamnan jihar Borno, Nana Shettima

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon zanga-zangar tunawa da 'yan matan Chibok shekaru biyu da sace su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016-
2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016- 2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel